Shugabar Jam'iyyar Adawa Ta Fadi Gaskiya kan Labarin Komawa SDP Tare da El Rufai

Shugabar Jam'iyyar Adawa Ta Fadi Gaskiya kan Labarin Komawa SDP Tare da El Rufai

  • Sanata Nenadi Esther-Usman ta karyata jita-jitar cewa ta fice daga jam’iyyar LP zuwa SDP mai adawa a Najeriya
  • Nenadi ta bayyana cewa shugaban SDP, Shehu Gabam, ne ya gayyace ta wajen tarban Nasir El-Rufai a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja
  • Ta jaddada cewa cikakken tsarin dimokuradiyya yana bukatar karfi da tasirin jam’iyyun adawa masu sa ido kan gwamnati
  • Ta bayyana cikakken biyayyarta ga jam’iyyar LP, tana mai cewa za su hada gwiwa da sauran yan adawa domin kyakkyawar shugabanci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugabar kwamitin riko na jam’iyyar LP, Sanata Nenadi Usman, ta yi martani kan jita-jitar komawarta SDP.

Sanata Nenadi Usman ta karyata rade-radin cewa ta koma jam’iyyar SDP bayan komawar Nasir El-Rufai.

Shugabar LP ta yi martani kan rade-radin komawarta SDP
Shugabar riko na jam'iyyar LP, Sanata Nenadi Usman ta ƙaryata labarin komawa SDP. Hoto: Sen. Nenadi Usman, Nasir El-Rufai.
Asali: Facebook

El-Rufai ya zargi APC da hargitsa jam'iyyun adawa

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Kalaman El Rufai sun jawo masa sabuwar matsala daga shiga SDP

Nenadi ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja ranar Laraba 12 ga watan Maris, 2025, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gan ta a wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta tare da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a wajen taro.

A cikin bidiyon, El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ce ke haddasa rikice-rikice da shari’o’i a jam’iyyun adawa.

Ya fadi hakan ne a lokacin da ya kai ziyara hedikwatar jam’iyyar SDP da ke Abuja, lamarin da ya haddasa surut.

Ganin Nenadi tare da El-Rufai ya sa mutane suka fara rade-radin cewa ta sauya sheka zuwa SDP daga LP.

Shugabar jam'iyyar adawa ta ƙaryata labarin bin El-Rufai zuwa SDP
Sanata Nenadi Usman ta musanta jita-jitar komawa jam'iyyar SDP da El-Rufai yake. Hoto: Nasir El-Rufai.
Asali: Twitter

Sanata Nenadi Usman ta fadi haduwarta da El-Rufai

Sanata Nenadi ta ce ta fitar da sanarwar ce domin wanke kanta daga jita-jitar da ke yawo a kafofin sadarwa.

Sanatar ta yi karin haske kan yadda ta samu kanta tare da El-Rufai da shugabannin jam’iyyar SDP a wancan lokacin.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tsage gaskiya shirtinsa na bin El Rufai zuwa SDP

Ta ce:

“Jiya, shugaban SDP, Alhaji Shehu Gabam, ya gayyace ni domin tarbar Mallam El-Rufai cikin gungun jam’iyyun adawa a Abuja.”
“Mallam ya yanke shawarar shiga adawa ne domin karfafa dimokuradiyya ta hanyar sa ido mai inganci a kan gwamnati.”
“Jam’iyyar adawa ba wai don su kalubalanci gwamnati kadai ba, har ma don su kare muradun al’umma da duba ayyukan gwamnati.”

Matsayar Nenadi Usman a jam'iyyar LP

Sanata Nenadi Usman ta kara da cewa tana nan daram a jam’iyyar LP kuma za su ci gaba da aiki tare da sauran ‘yan adawa.

Ta kara da cewa:

“Jam’iyyar LP ta kuduri aniyar bunkasa adawa mai karko domin samar da cigaba da jin dadin al’umma a kasa.”
“Muna maraba da kowane dan siyasa mai gaskiya da kishin kasa da son ganin an kawo sauyi a Najeriya.”

Gwamna Alia ya ƙaryata labarin komawa SDP

Kun ji cewa Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya mayar da martani kan raɗe-raɗin da ke cewa yana shirin ficewa daga jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Manyan ƴan siyasa, jam'iyya da El-Rufai ya ziyarta kafin yanke shawarar barin APC

Gwamna Alia ya musanta cewa yana shirin bin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai zuwa jam'iyyar SDP mai adawa a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel