"Da Shi Muka Shirya Yaƙar Atiku," Wike Ya Tona Asirin Gwamna a Arewacin Najeriya
- Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya yi ikirarin cewa Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya ci amanarsu a zaɓen 2023
- Wike ya ce sai da suka gama magana da Bala cewa za su haɗu su yaƙi Atiku Abubakar, amma daga baya ya zagaye ya koma bayansa
- A cewarsa, da yawan gwamnonin PDP suna yaƙar jam'iyya a ɓoye amma ba za su iya nunawa ba, ya ce idan suka musa zai fallasa su
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana yadda rikicin cikin gida ya durkusar da jam’iyyar PDP tun kafin zaɓen 2023.
Mista Wike ya kuma zargi gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, da cin amanaar tawagar gwamnonin G-5 waɗanda suka yaki Atiku Abubakar a 2023.

Asali: Twitter
Ministan ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai da ya yi ranar Talata, 12 ga watan Maris, 2025, kamar yadda Leadership ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya sake jaddada cewa gwamnonin PDP da dama sun yi aiki a ɓoye don rusa jam’iyyar, musamman a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
"Ni na kare yunkurin rusa PDP" - Wike
Wike ya tuno da yadda jam’iyyar PDP ta fuskanci barazana a lokacin ya na a matsayin gwamnan jihar Ribas.
Tsohon gwamnan ya ce:
“Lokacin da nake gwamna, na gano jam’iyya mai mulki na amfani da Ali Modu Sheriff don rushe PDP. Na tsaya tsayin daka don kare jam’iyyar. Ban taɓa zuwa Aso Villa don cin amanar jam’iyya ba.”
Wike ya bayyana cewa PDP ba za ta iya shirya kanta gabanin babban zaɓe na gaba ba, yana mai cewa:
“Kowane gwamna da kuke gani a PDP yana aiki ne da nufinsa, yana yi wa jam’iyyar zagon ƙasa, idan kuma sun musa, zan fallasa su.”
Zargin Gwamna Bala da cin amana
Ministan ya bayyana cewa Bala Mohammed ya nemi taimakon gwamnonin G5 domin yaƙi da Atiku Abubakar a zaɓen 2023, amma daga baya ya juya musu baya.

Kara karanta wannan
2027: Yan adawa na shirin firgita Tinubu, ƙusa a PDP ya ce guguwar canji za ta tafi da APC
A rahoton Daily Trust, Wike ya kara da cewa:
"Gwamna Bala ya samu saɓani da Atiku da tawagarsa. Lokacin da zai zo jihar Ribas, na ce masa ya jira ni a filin jirgi. Ya ce mani Atiku zai hallaka shi idan ya ci zaɓe, don haka dole mu mara wa Asiwaju baya.
"Muka tattaru gaba ɗaya muka je Bauchi don nuna goyon baya, sai dai daga baya muka gane cewa ya yi amfani da mu ne kawai don sasantawa da Atiku.”
“Bayan mun baro Bauchi, sai Tambuwal ya jagoranci wata tawaga zuwa wurinsa, nan take ya juya mana baya.”
Wike ya ce Majalisa za ta iya tsige Fubara
A wani labarin, kun ji cewa Wike ya bukaci Majalisar Dokokin jihar Ribas su tuge Gwamna Simi Fubara matuƙar ya aikata laifin da ya cancanci hakan.
Tsohon gwamnan kuma ministan Abuja na yanzu, ya koka da yadda rikicin ya ki karewa, yake zargin wasu da ci gaba da ruruta rigimar domin biyan buƙatar kansu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng