Bayan Rasa El Rufai, Gwamnatin Tinubu Ta Fadi 'Dan Takarar Shugaban Kasa da Zai Dawo APC

Bayan Rasa El Rufai, Gwamnatin Tinubu Ta Fadi 'Dan Takarar Shugaban Kasa da Zai Dawo APC

  • Hadimin shugaba kasa, Daniel Bwala ya ce dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi zai bar jam'iyyarsa ya koma APC kafin zaben 2027
  • Bwala ya ce sauya shekar Valentine Ozigbo da Balami alamu ne na faduwar jam’iyyar LP da ta zo ta uku a zaben karshe da aka yi
  • Daniel Bwala ya bayyana cewa Obi ba zai sake takarar shugaban kasa a ƙarƙashin LP ba domin zai sauya sheka zuwa APC mai mulki
  • Mai taimakawa shugaban kasar ya soki yunkurin kafa kawance da SDP, yana cewa rikici zai barke tsakaninsu saboda shugabanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Daniel Bwala, mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan sadarwa da manufofi ya yi magana kan zaben 2027.

Barista Daniel Bwala ya tabbatar da cewa Peter Obi zai watsar da LP domin shiga jam’iyyar APC nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Manyan 'yan siyasar Arewa sun fara lallaba Jonathan, ana son ya nemi kujerar Tinubu

Hadimin Tinubu ya fadi lokacin da Obi zai dawo APC
Daniel Bwala ya ce saura kiris Peter Obi ya dawo APC. Hoto: Peter Obi, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Yaushe Peter Obi zai dawo jam'iyyar APC?

Bwala ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na TVC da ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba 12 ga watan Maris din shekarar 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daniel Bwala ya ce shugaban kasa da jam’iyyar APC na samun nasara wajen fitar da mambobi daga LP, har ya kawo misalin Ozigbo da Balami.

Ya ce shigowar Ozigbo APC alama ce da ke nuna cewa Peter Obi shi ma yana dab da sauya sheka zuwa jam’iyyar da ke mulkin Najeriya.

Daniel Bwala ya ce:

“Kun san muna kwashe ƴan jamiyyar LP? Ba wai muna kiransu ne ba, Suna zuwa da kansu, Valentine Ozigbo ya shigo, Balami ya shigo.
"Har Peter Obi ma zai shigo kafin 2027, wannan dama muna samun nasara ne, Peter Obi ba zai tsaya takara a LP ba, Duka za su bar jam'iyyarsu."
Bwala ya yi hasashen SDP za ta tsunduma cikin rikici
Daniel Bwala ya soki shirin haɗaka da ake yi musamman a jam'iyyar SDP. Hoto: Nasir El-Rufai, Bwala Daniel.
Asali: Facebook

SDP: Bwala ya hango rigima a jam'iyyar El-Rufai

Kara karanta wannan

An fara: Tsohon ministan Buhari ya goyi bayan tafiyar El Rufa'i a jam'iyyar SDP

Daniel Bwala ya ce Peter Obi ba zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin LP ba, domin zai koma jam’iyyar APC.

Ya kara da cewa:

“Valentine Ozigbo ya shigo jam’iyyarmu, Kuma shi ne ke da kusanci da Obi sosai, don haka na tabbata Obi zai biyo bayansa.”

Bwala ya ce yana da shakku kan tasirin hadin gwiwar da ‘yan adawa ke yi da SDP, yana ganin rikice-rikice za su hana su samun nasara.

A cewarsa:

“Suna shirya abubuwa ne yadda kowanne mako zaka ji wani babban dan siyasa ya koma SDP don kawai a janyo hankalin kafafen yada labarai.
“Sun fi mayar da hankali kan jan hankalin jama’a ta kafafen labarai, amma bayan hakan, rikici zai barke tsakaninsu.
“Za su fara rikici ne kan wanene zai zama shugaba, wanene mataimaki, da kuma wanene zai rike madafun iko.”

'Dalilin sukar Tinubu a baya' - Daniel Bwala

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa ta yi magana kan sauya sheƙar El Rufai daga APC zuwa SDP

Kun ji cewa mai bai wa shugaban kasa shawara kan yada labarai da tsare-tsare, Daniel Bwala ya bayyana abin da ya sa shi sukar Bola Tinubu.

Daniel Bwala ya kare kansa, yana mai cewa jam’iyyar adawa tana da hakkin sukar gwamnati mai mulki domin tabbatar da an dora ta kan hanya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel