Bayan Kama Layin Uba Sani, Sanata Ya Fadi Dalilin Faduwarsa a Zaben 2019
- Shehu Sani ya ce ya rasa kujerar Sanata a 2019 ne saboda ya ki amincewa da bashin dala miliyan 340 da Nasir El-Rufai ya yi niyyar ciyowa
- Shehu Sani ya bayyana cewa gwamna da ‘yan majalisar jiha sun ki amincewa da shi, amma yanzu gaskiyarsa ta bayyana fili
- Ya ce bashin ya hana ci gaban jihar, ya bar ayyuka barkatai ba a kammala su ba, ya sa Kaduna ta zama jiha ta biyu mafi bashi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Sanata Shehu Sani, tsohon dan majalisar dattawan Kaduna, ya ce ya rasa kujerarsa a 2019 saboda ya kalubalanci yunkurin Nasir El-Rufai na daukar bashi.
Shehu Sani ya fadi haka ne yayin da ya jaddada goyon bayansa ga Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna da kuma zaben 2027.

Source: Facebook
'Dalilin rasa kujera ta ta Sanata' - Shehu Sani
Sanata Shehu Sani ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai a Abuja, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehu Sani ya ce ya nace wajen fadin gaskiya koda kuwa hakan zai sa a kore shi ko kuma ya rasa wani abu a rayuwarsa.
Shehu Sani ya ce:
"Na dage wajen fadin gaskiya ga masu mulki, kuma wannan ne yasa na rasa kujerata a 2019.
“El-Rufai yana neman bashin dala miliyan 340, amma muka ce a'a, saboda hakan zai kawo illa ga mutanenmu.
“Mun gaya masa hakan ba zai amfanar da jihar ba, amma ya ci gaba da kokarinsa, kuma ya dauke mu a matsayin abokan gaba.”
Sanatan ya ce wannan rikicin siyasa da El-Rufai ya shafi wasu ‘yan siyasa da dama, wanda ya sa suka fice daga jam’iyyar APC gaba daya.
Sani ya kara da cewa:
“Na tsaya da gwamna, na kuma biya farashin hakan ta rasa kujerata, amma yau na ga an tabbatar da gaskiyata.
“A lokacin, gwamna, ‘yan majalisar jiha da sauran ‘yan siyasa sun ki amincewa da ni, amma yanzu gaskiyata ta bayyana a fili.

Source: Facebook
Sani ya fadi musabbabin rasa kujerun yan majalisa
Shehu Sani ya ce yana alfahari da irin matsayin da ya dauka a lokacin da ake magana akan bashin da bai amfani jihar ba.
A cewarsa:
“Ina jin dadin cewa, idan na mutu, babu wanda zai ce ni ne na sa hannu kan bashin da za a biya har shekaru 100.
“Gaskiya da na tsaya akai ta fi komai mahimmanci a gare ni, fiye da dawowata majalisar tarayya."
Ya ce dalilin da yasa yawancin ‘yan majalisa ba sa dawowa shi ne saboda rashin biyayya ga gwamnoni a jihohinsu wanda hakan yake zama musu barazana a siyasa.
Shehu Sani ya fadi dalilin komawa APC
Kun ji cewa kwanaki bayan komawarsa jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kaduna, Shehu Sani ya fito ya gayawa duniya dalilinsa na yin hakan.
Tsohon sanatan na Kaduna ya bayyana cewa ko a baya wasu dalilai ne suka sanya ya yi murabus daga jam'iyyar wacce da shi aka kafa ta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

