Bauchi: Sanata Ya Gagara Boye Kwadayin Takarar Gwamna, Ya Roki Shugabannin PDP

Bauchi: Sanata Ya Gagara Boye Kwadayin Takarar Gwamna, Ya Roki Shugabannin PDP

  • Ahmed Abdul Ningi ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Bauchi a 2027 karkashin PDP, bayan ganawa da shugabannin jam’iyya
  • Sanata Ningi ya ce ba yana son shahara ba ne, amma yana da burin ci gaba da yi wa jama’a hidima da cikakken nauyi da girman mukami a Bauchi
  • 'Dan siyasar ya jaddada cewa shi dan PDP ne tun daga kafuwar jam’iyyar, kuma yana da burin tabbatar da cewa jam’iyyar ta ci gaba da mulki
  • Ya bukaci shugabannin jam'iyyarsu ta PDP su tabbatar da cewa dan takarar gwamna a 2027 ya cancanta, yana da karfin da iya cin zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Sanatan da ke wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Ahmed Abdul Ningi, ya bayyana kudurinsa na tsayawa takarar gwamnan Bauchi a 2027.

Sanata Abdul Ningi ya bayyana aniyarsa, ya ce yana sha'awar tsayawa takara karkashin jam’iyyar adawa ta PDP mai adawa a Najeriya.

Kara karanta wannan

2027: Ministan Tinubu ya nuna sha'awar tsayawa takarar gwamna

Sanata ya bayyana aniyarsa ta neman takarar gwamna a 2027
Sanata Abdul Ningi ya nuna sha'awar takarar gwamna a Bauchi. Hoto: Ahmed Abdul Ningi.
Asali: Facebook

Sanata zai nemi takarar gwamna a zaɓen 2027

A ranar Juma’a ne Abdul Ahmed Ningi ya sanar da hakan yayin wata ganawa da shugabannin jam’iyyar PDP, cewar jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Ningi ya fadi haka ne a taron da shugabannin jam'iyyar a karamar hukumar Ganjuwa, daya daga cikin yankunan Bauchi ta Tsakiya da yake wakilta.

Sanatan ya bayyana cewa ya yanke shawarar tsayawa takarar ne domin amsa kiran da ake yi masa a cikin jam’iyya, wanda ya kasance cikakken mamba tun farko.

Sanata ya kwadaitu da kujerar gwamna a 2027
Sanata Abdul Ningi ya fadi niyyarsa kan takarar gwamna a Bauchi a zaben 2027. Hoto: @NGRSenate.
Asali: Twitter

Menene dalilin neman takarar gwamna da zai yi?

Sai dai Ningi ya jaddada cewa ba don neman suna ko daukaka ba yake son takara, amma don ci gaba da hidimtawa al’ummar jihar Bauchi gaba daya.

Ya ce:

“Ba don neman suna ko daukaka nake neman gwamna ba, na riga na zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Me kuma nake bukata?”
“Tun daga kafuwar PDP nake cikinta, ban taba barin jam’iyyar ba, kuma ba zan taba barinta ba, muna nan don gina ta.”

Kara karanta wannan

Me ke faruwa da PDP? An rufe siyar da fom na takarar gwamna, babu wanda ya siya

Wani roko Sanata ya yi ga shugabannin PDP?

Ya bukaci shugabannin PDP su shirya don 2027, su tabbatar da cewa wanda zai samu tikitin takarar gwamna mutum ne da ke da karfi da cancanta, cewar Daily Post.

Shugabannin PDP sun yaba wa Ningi bisa gudunmawar da ya bayar tun daga shigowarsa siyasa, kuma sun tabbatar masa da cikakken goyon bayansu.

Hakan na zuwa ne yayin da gwamna mai ci, Sanata Bala Mohammed ke wa'adinsa na karshe kan mulkin jihar inda zai ba wasu dama a zaben 2027 mai zuwa.

Gwamna Bala ya goyi bayan Sanata Ningi

A baya, kun ji cewa bayan dakatar da Sanata Abdul Ningi, gwamnatin jihar Bauchi ta yi martani kan lamarin da ya faru ga sanatan.

Gwamna Bala Mohammed na jihar ya ce ya na tare da Ningi a kowane lokaci musamman idan abin da ya ke kai gaskiya ne.

Kara karanta wannan

Tirƙashi: PDP ta kori tsohon shugaban majalisar dattawa, an fadi zunubinsa

Gwamnan ya bayyana haka a ranar Laraba 13 ga watan Maris 2024 yayin taron majalisar zartarwar jihar a birnin Bauchi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.#

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng