Yadda Karasa Hako Fetur a Arewa zai ba Tinubu Nasara a 2027

Yadda Karasa Hako Fetur a Arewa zai ba Tinubu Nasara a 2027

  • Tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya amince da karasa hako man fetur a jihar Bauchi
  • Yakubu Dogara ya ce idan Tinubu ya amince da hakan tare da kammala gina madatsar ruwan Bagel-Zungur, ba zai bukaci kamfen ba a 2027
  • Sanata Shehu Buba ya kaddamar da titin da ya gina a Zaranda, ya ce hakan na cikin shirinsa na ci gaban mazabar Bauchi ta Kudu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta amince da cigaba hako man fetur a Bauchi.

Yakubu Dogara ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da wata hanya da Sanata Shehu Buba ya gina a yankin Zaranda da ke karamar hukumar Toro.

Kara karanta wannan

Tsohon Jigo a APC, Dr. Bugaje ya yi wankin babban bargo ga Buhari, Tinubu da APC

Dogara
Dogara ya bukaci cigaba da hako fetur a tsakanin Bauchi da Gombe. Hoto: Bayo Onanuga|Yakubu Dogaro
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Dogara ya ce idan aka aiwatar da aikin kafin 2027, Tinubu ba zai bukaci yakin neman zabe ba a Bauchi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2027: Me zai sa a zabi Tinubu a Bauchi?

Tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya amince da cigaba da hako man fetur a tsakanin Bauchi da Gombe.

Yakubu Dogara ya ce hakan zai inganta tattalin arzikin yankin tare da kawo ci gaba ga mazauna jihar.

Dogara ya kuma bukaci Tinubu da ya samar da kudi domin fara aikin gina madatsar ruwan Bagel-Zungur da aka jima ana jiran fara aikinsa.

A cewarsa, idan aka kammala wadannan ayyuka, Tinubu ba zai bukaci kamfen a Bauchi ba domin ayyukansa za su sanya a zabe shi cikin sauki.

Dogara ya yaba da kokarin Tinubu

Yakubu Dogara ya jinjina wa Shugaba Tinubu bisa irin kokarin da yake yi domin bunkasa tattalin Najeriya.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Gwamna ya bukaci jiragen yaki su rika sintiri a iyakokin Bauchi

Ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na da rawar da za ta taka wajen tabbatar da cewa jihar Bauchi ta ci gajiyar mulkin Tinubu.

Ya ce a matsayinsu na ‘yan Bauchi, za su ci gaba da mara wa Tinubu baya idan ya aiwatar da samar da man fetur da madatsar ruwa.

Leadership ta wallafa cewa Dogara ya yi kira ga shugabanni da su yi amfani da mulki wajen kawo cigaba ba wai don biyan bukatar siyasa kadai ba.

Sanata ya kaddamar da hanya a Bauchi

A yayin taron, Sanata Shehu Buba ya kaddamar da titin kilomita 2.5 da ya gina a Zaranda, da ke karamar hukumar Toro.

Ya bayyana cewa aikin yana daga cikin shirinsa na inganta hanyoyi domin saukaka zirga-zirgar jama’a da bunkasa kasuwanci.

Sanata Buba ya ce hanyar alkawari ne da ya dauka lokacin kamfen, kuma yanzu ya cika alkawarin ga mutanensa.

Kara karanta wannan

Tinubu ba ya cikin Najeriya yanzu haka, an ji inda shugaban kasar ya tafi

Ya ce aiki na daya daga cikin shirye-shiryen ci gaban mazabarsa, yana mai alkawarin ci gaba da ayyuka masu amfani.

An zargi 'yan APC da hada kai da PDP

A wani rahoton, kun ji cewa wata kungiya mai goyon bayan shugaba Bola Tinubu ta ce ba abin da zai hana shi sake lashe zabe a 2027.

Kungiyar ta ce Bola Tinubu yana aiki tukuru kuma ba zai ji shakkar haduwar 'yan adawa ba, ta kuma zargi wasu 'yan APC da yin makarkashiya ga Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng