Da duminsa: Buhari ya kaddamar da hakar man fetur a tsakanin Bauchi da Gombe

Da duminsa: Buhari ya kaddamar da hakar man fetur a tsakanin Bauchi da Gombe

- Buhari ya kaddamar da fara hakan/tonon iskar gas, da danyen man fetur na Kolmani da ke karamar hukumar Alkeri da ke jihar Bauchi

- Buhari ya yi nuni da cewa kasar na samun kudaden kasafin kudi daga iskar gas da man fetur, haka zalika tattalin arziki na bunkasa daga ma'adanan

- Babban daraktan NNPC, Dr. Maikanti Baru ya ce NNPC tare da hadin guiwar wani kamfanin kasar China sun gano man fetur da iskar gas mai yawa a garin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da fara hakan/tonon iskar gas, da danyen man fetur na Kolmani da ke karamar hukumar Alkeri da ke jihar Bauchi.

Da ya ke kaddamar da hakar man a kauyen Burumbu da ke karamar hukumar Alkaleri, shugaban kasa Buhari ya yi nuni da cewa iskar gas da danyen mai har yanzu sune manyan bangarorin da kasar ke samun kudaden kaddamar da kasafin kasar da kuma habbaka tattalin arziki.

Shugaban kasar ya bayyana cewa ya dauki sha'awar fadada bincike kan samar da man fetur a lokacin da yake rike da mukamin kwamishinan albarkatun kasa na tarayya a 1960, amma cikin rashin dace, aka dakatar da hakan bayan shekaru biyu, a lokacin mulkin Obasanjo.

KARANTA WANNAN: Yanzunnan: Dandanzon jama'a sun halarci kaddamar da yakin zaben Buhari a Gombe

Da duminsa: Buhari ya kaddamar da hakar man fetur a tsakanin Bauchi da Gombe
Da duminsa: Buhari ya kaddamar da hakar man fetur a tsakanin Bauchi da Gombe
Asali: Facebook

Ya yi amfani da damar wajen yin godiya ga kamfanin NNPC bisa namijin kokarinsu na ganin aikin hakar mai a wajen ya kankama cikin kankanin lokaci.

Tun farko, gwamnan jihar Bauchi Mumammad Abdullahi Abubakar ya bayyana jin dadinsa kan yadda har aikin hakar mai a jihar ya kai wannan matsayi, tare da jinjinawa shugaban kasa Buhari na fara assasa aikin.

Babban daraktan NNPC, Dr. Maikanti Baru ya ce NNPC tare da hadin guiwar wani kamfanin kasar China sun gano man fetur da iskar gas mai yawa a garin, domin haka ne ya bayyana bukatar gaggauta fara hakar ma'adanan.

Shugaban kasar ya samu rakiyar gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abubakar, tare da takwaransa na jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ministoci da kuma manyan jami'an gwamnati.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel