Dandazon Jama'a Sun Tarbi Buhari da Ya Fito Zabe na Farko bayan Gama Mulki
- Tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya kada kuri’arsa a Daura, yayin da jama’a suka fito domin zaben shugabannin kananan hukumomi
- Gwamna Dikko Radda ya jinjinawa yadda aka gudanar da zaben cikin lumana, yana mai cewa dimokuradiyya ta samu karbuwa a Katsina
- Gwamnatin jihar ta ce za a samar da tsaro da adalci a zaben, inda ta yabawa hukumar SIEC da hukumomin tsaro bisa shirin da suka yi na yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - A yau, tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kada kuri’arsa a garin Daura yayin zaben shugabannin kananan hukumomi na Jihar Katsina.
Zaben ya gudana ne a fadin jihar, inda jama’a suka fito don zaben shugabanni a matakin kananan hukumomi.

Asali: Twitter
Mai magana da yawun gwamnatin Katsina, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook cewa gwamna Dikko Umaru Radda, ya kada kuri’arsa a karamar hukumar Charanchi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar gwamnan, gwamnati ta dauki matakan kare sahihancin zaben, tare da tabbatar da tsaro domin baiwa kowa damar kada kuri’a ba tare da tsangwama ba.
Muhammadu Buhari ya kada kuri’a a Daura
Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya kada kuri’arsa a rumfar zabe ta 003 da ke Sarkin Yara, Gundumar A, a garin Daura, Jihar Katsina.
Buhari ya kada kuri’arsa ne tare da Kwamishinan Harkokin Musamman na Jihar Katsina, Adnan Na-Habu Daura, da misalin karfe 11:09 na safiyar yau.
Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya wallafa hotunan yadda mutane suka yi tururuwa yayin da tsohon shugaban kasar ya fito kada kuri'a a shafinsa na X.
Gwamnan Katsina ya yabi yadda aka fito zabe
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Ummaru Radda, ya kada kuri’arsa a rumfar zabe ta 010, Barebari A, da ke Radda, Karamar Hukumar Charanchi.
Bayan kada kuri’arsa, Gwamna Radda ya jinjinawa yadda jama’a suka fito cikin nutsuwa da bin doka domin kada kuri’arsu.
Dikko Radda ya ce:
“Yawan jama’ar da suka fito da kuma yadda suke gudanar da zabe cikin tsari yana nuna cewa dimokuradiyya ta samu karbuwa."
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare ‘yancin masu kada kuri’a, yana mai cewa:
“Shugabannin da za su fito daga wannan zabe su ne za su wakilci ra’ayin al’umma.”
Gwamna Radda ya ce za a yi sahihin zabe
Gwamna Radda ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta dauki tsauraran matakan tabbatar da gaskiya da adalci a zaben kananan hukumomin.
A cewarsa:
“An samar da shirye-shirye na musamman don tabbatar da cewa dukkanin sassan jihar sun samu damar kada kuri’a ba tare da wata matsala ba.”
Gwamnan ya yabawa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Katsina (SIEC), hukumomin tsaro, da masu sa-ido kan zabe bisa yadda suka tabbatar da tsaro da ingancin zaben.
“Matakan da SIEC, hukumomin tsaro da masu sa-ido suka dauka za su tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zabe ba tare da cin zarafin masu kada kuri’a ba.”
- Dikko Radda
Usman Bugaje ya yi magana kan mulkin Buhari
Tsohon jigo a APC, Dr Usman Bugaje ya yi tsokaci kan yadda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafiyar da mulkinsa.
Haka zalika Dr Usman Bugaje ya ce yadda Muhammadu Buhari ya lalata lamura, haka Bola Tinubu ya dauko hanyar ruguza tattalin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng