An Fara Juyawa Tinubu, Atiku da Peter Obi Baya game da Zaben Shugaban Ƙasa na 2027
- Tsohon jigon jam'iyyar LP, Kenneth Okonkwo ya bukaci shugaban ƙasa, Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi su hakura da takara a 2027
- Okonkwo ya ce lokaci ya yi da waɗannan manyan ƴan siyasar za su matsa gefe, su ba matasa dama a ƙasar nan
- Fitaccen jarumin Nollywood, wanda ya bar LP kwanan nan ya ce ba zai koma jam'iyyar APC ba har sai idan ta gyara manufofinta
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon dan jam’iyyar LP, Kenneth Okonkwo, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu, Peter Obi, da Atiku Abubakar, su haƙura da takarar shugabancin kasa a zaben 2027.
Okonkwo, wanda tsohon kakakin yakin neman zaben LP ne a 2023, ya goyi bayan Obi a lokacin, amma yanzu ya sauya ra’ayi, yana mai cewa lokaci ya yi da za a bai wa sabbin ‘yan takara dama.

Source: Facebook
Ɗan siyasar ya faɗi haka ne a wata hira da tashar Channels Television a shirin siyasa a yau ranar Talata, 11 ha watan Fabrairu, 2025.
Ya kamata Tinubu, Atiku, Obi su haƙura
Da aka tambaye shi ko yana kan bakarsa na cewa su Tinubu, Obi da Atiku su janye daga takara, tsohon jigon LP ya ce:
“Na fada kuma ina nan a kan bakata saboda a Najeriya, idan mutane sun ba ka dama, dole ne ka dauki nauyin kare ta, ba zai yiwu ka yi sakaci da amanar jama'a ba.
"Ya zama dole ka yi duk abin da ya kamata wajen kare ƙasar. Abin takaici ne cewa a kasar nan ba wai kawai samun kuri’u ke da muhimmanci ba, dole ne ka yi dagaske wajen karɓar haƙƙinka.
Okonkwo ya daina goyon bayan Obi
Tsohon dan jam’iyyar LP din ya kara da cewa duk abin da ya faru a 2023 ya wuce, kuma bai da shirin mara wa Obi baya a gaba.
“Har yanzu ina kan bakata. Duk abin da ya faru a 2023 ya kamata a bar shi a 2023,” in ji shi.
Jarumin Nollywood zai koma APC
Okonkwo, wanda ya yi fice a masana’antar shirya fina-finai ta Nollywood, ya fice daga LP ne a ranar Talata, yana mai cewa rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar ne suka sa ya yanke wannan shawara.
Ya kuma bayyana cewa ba zai koma jam’iyyar APC ba, wacce ya bari a baya saboda wahalhalun da yake zargin ta kawo a kasar nan.
“Ina tabbatar muku da cewa, zan zama mutum na farko da zai karbi APC idan ta canza halayenta ta zama jam’iyyar da ke yi wa ‘yan Najeriya aiki,” in ji shi, yana mai zargin APC da gazawa wajen magance matsalolin kasar.
Ganduje ya kore dawowar mulki Arewa a 2027
A wani labarin, kun ji cewa shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya bukaci ƴan siyasar Arewa su haƙura da batun takarar shugaban ƙasa a 2027.
Ganduje ya ce mulki ba zai koma Arewa ba sai shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya gama shekaru takwas, watau a 2031.
Asali: Legit.ng

