2027: Kashim Shettima Ya Fadi Yadda Ya ke Mu'amalantar Atiku a Bayan Fage

2027: Kashim Shettima Ya Fadi Yadda Ya ke Mu'amalantar Atiku a Bayan Fage

  • Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya fadi yadda ya ke girmama Atiku Abubakar, har yana kiran sa Baba
  • Shettima ya bayyana hakan ne a wani taro da aka shirya domin tunawa da cikar Dr. Kayode Fayemi shekara 60 a duniya
  • Atiku Abubakar ya kasance cikin manyan 'yan siyasa da suke hamayya sosai da gwamnatin Bola Tinubu a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa zai ci gaba da jefa wa Atiku Abubakar kalubale a siyasa duk da girmamawa da yake masa a matsayin dattijo.

Kashim Shettima ya bayyana hakan ne cikin dariya a yayin wani taron tunawa da cikar tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, shekara 60 da haihuwa a Abuja.

Kara karanta wannan

Rusau: Abba zai kashe biliyoyi wajen yin asibiti, tituna, lantarki a Rimin Zakara

Shettima
Mataimakin shugaban kasa ya yi kira ga shugabanni su hada kai. Hoto: Kashim Shettima|Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Kashim Shettima ya bukaci shugabanni su hada kai domin kawo cigaba duk da bambancin jam'iyyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ya Kashim Shettima ke mu'amala da Atiku?

A yayin jawabin sa, Shettima ya tuna yadda ya rika sukar Atiku a zaben 2023, yana harba masa zafafan maganganu saboda siyasa.

Sai dai ya ce Atiku ya dauki sukar da salama, saboda haka yana masa kallon dattijo, wanda a tattaunawa ta bayan fage yake kiransa da "Baba".

Bayan Shettima ya ce zai cigaba da sukar Atiki da maganganu a 2027 duk da girmamasa da ya ke, mahalarta taron sun fashe da dariya, wanda hakan ya sanya Atiku murmushi.

Yadda Atiku ke sukar gwamnatin Tinubu

A kwanan nan, Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin shugaba Bola Tinubu da kokarin rage karfin jam’iyyun hamayya domin hana su yin tasiri a siyasa.

Atiku ya ce gwamnatin Tinubu na amfani da kudi wajen lalata jam’iyyun hamayya, yana mai cewa an raba miliyoyin Nairori ga wasu jam’iyyun siyasa don su rabu da adawa.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Tinubu ya bayyana babban abin da ya saka a gaba a Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa lokaci ya yi da ‘yan adawa za su hada kai domin hambarar da gwamnatin Tinubu a zaben 2027.

Ya bukaci shugabannin hamayya su yi hadin gwiwa don samar da hadakar da za ta iya kawar da APC daga mulki a 2027.

Shettima ya bukaci a hada kai

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bukaci shugabanni su hada kai don ci gaban Najeriya, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba.

Ya ce makomar nahiyar Afrika ta dogara ne kan nasarar Najeriya, saboda haka ya zama dole shugabanni su yi aiki tukuru don amfanin al’umma.

Kashim Shettima ya roki shugabanni da su mayar da hankali kan cigaban kasa, maimakon rikice-rikicen siyasa da zai iya jefa kasar cikin matsala.

Ayyukan da Tinubu ya yi a Janairu

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu ta zartar da wasu ayyuka na musamman a farkon shekarar 2025.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 6 da Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya a watan farko na 2025

Legit ta rahoto cewa gwamnatin Bola Tinubu ta yi wasu muhimman ayyuka shida a watan farko na 2025 ciki har da sauya fasalin shirin N-Power na matasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng