A Hukumance, Jam'iyyar APC Ta Samu Ƙarin Sanata 1 a Majalisar Dattawan Najeriya

A Hukumance, Jam'iyyar APC Ta Samu Ƙarin Sanata 1 a Majalisar Dattawan Najeriya

  • Sanata mai wakiltar al'ummar mazaɓar jihar Delta ta Arewa, Ned Nwoko ya sauya sheƙa a hukumance daga PDP zuwa APC mai mulkin ƙasar nan
  • Hakan na kunshe ne a wata wasiƙa da shugaban Majalisar Dattawa, Godwill Akpabio ya karanta a zaman sanatoci yau Laraba a birnin tarayya Abuja
  • Shugaban masu rinjaye na Majalisar dattawa, Sanata Bamidele ya nuna farin cikinsa, inda aka ga yana ɗaga hannun Owoko tare da wasu sanatocin APC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - A hukumance, jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta samu ƙarin sanata ɗaya a majalisar dattawan Najeriya.

Sanata Ned Munir Nwoko mai wakiltar jihar Delta ta Arewa ya tabbatar da sauya sheƙarsa daga PDP zuwa jam'iyyar APC a hukumance yau Laraba, 5 ga watan Fabrairu, 2025.

Sanata Ned Nwoko.
Sanata Ned Nwoko ya fice daga PDP zuwa APC a hukumance a Majalisar dattawa Hoto: @mob_sen_leader
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa hakan na ƙunshe ne a wasiƙar canza jam'iyya da sanatan ya miƙawa Majalisar Dattawa.

Kara karanta wannan

"Me suke shiryawa?": Ziyarar da Atiku Abubakar ya kai wa Sanata Binani ta bar baya da ƙura

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nwoko ya lashe kujerar sanatan Delta ta Arewa ne a zaɓen 2023 karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Majalisa ta tabbatar da sauya shekar Sanata Nwoko

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya karanta wasikar sauya shekar Ned Nwoko zuwa jam’iyyar APC a zaman sanatoci na yau Laraba.

A cikin wasikar, Nwoko ya danganta matakin da ya dauka da rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP a jihar Delta.

Sanatocin APC sun ɓarke da murna a majalisa

A wasu hotuna da shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Michael Opeyemi Bamidele ya wallafa a shafinsa na X, ya nuna yadda suka yi murna da ci gaban.

Sanata Bamidele ya bayyana cewa ya taka muhimmiyar rawa wajen tarbar Sanata Nwoko zuwa cikin jam'iyyar APC.

Hotunan sun nuna yadda sanatocin APC suka tashi suna ɗaga hannun Ned Nwoko domin murnar shigowarsa cikinsu a jam'iyya mai mulki.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, Sanata Orji Uzo Kalu da Bamidele na cikin waɗanda aka gani suna murnar sauya sheƙar Nwoko.

Kara karanta wannan

"Akwai matsala": Majalisar amintattun PDP ta shiga taron gaggawa a Abuja

APC ba ta bukatar gwamnan Delta ya dawo cikinta

A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege ya ce suna maraba da duk wanda zai shiga APC a Delta amma ban da mutum biyu.

Sanata Omo-Agege ya ce jam'iyyar APC ba ta buƙatar Gwamna Sheriff Obrevwori da magabacinsa, Ifeanyi Okowa a cikinta, ya buƙaci su yi zamansu a PDP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel