Bayan Ganawa da Tinubu, APC Ta ba Gwamnan PDP Wa'adi game da Gayyatarsa Jam'iyya
- Ƙungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya ta sake gayyatar gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya fice daga PDP ya shiga jam’iyyarta domin samun karin damar ci gaba
- Sanarwar da Saleh Zazzaga ya fitar ta bayyana cewa shiga APC zai ba Mutfwang damar jagorantar jam’iyyar a jihar Filato gabanin taron jam’iyyar
- Ƙungiyar ta jaddada cewa shiga APC zai kara haɗin kai tsakanin Mutfwang da Shugaba Bola Tinubu, tare da tabbatar da cigaban jihar Filato
- Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Caleb Mutfwang ya yi wata ganawa da Mai girma Bola Tinubu a Lagos makwanni uku da suke wuce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jos, Plateau - Ƙungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya ta sake kira ga gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya dawo jam'iyya mai mulkin Najeriya.
Kungiyar ta bukaci Mutfwang ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC domin kara samun damarmaki na kawo ci gaba a jiharsa.

Asali: Twitter
Menene Gwamna Caleb ya tattauna da Tinubu?
Sanarwar da shugaban ƙungiyar, Saleh Zazzaga, ya fitar a Abuja, ta bukaci Mutfwang ya shiga APC kafin taron jam’iyyar mai zuwa, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ya biyo bayan Caleb Mutfwang ya gana da Bola Tinubu inda ya ce an samu gagarumin ci gaba a yanayin tsaro a jihar daga Janairu zuwa Disambar 2024.
Gwamnan ya ce Shugaba Bola Tinubu ya bayar da gudunmawa sosai kuma yana da jajircewa wajen inganta tsaro a jihar.
Mutfwang ya yi wannan tsokaci ne lokacin da ya ziyarci Tinubu a gidansa da ke Bourdillon, jihar Legas, a ranar 28 ga Disamba.
Kungiyar APC ta roki gwamna Caleb ya bar PDP
Wannan gayyata na zuwa ne ganin nasarorin gwamnan ke samu a mulki da kuma kudurin jam’iyyar na karfafa haɗin kai.
Saleh Zazzaga ya kuma tabbatar da cewa komawar gwamnan APC zai ba shi damar zama jagoran jam’iyyar a jihar Plateau.
Sanarwar ta kara jaddada cewa shiga APC zai sa gwamnan ya samu karin damar aiki kafada da kafada da Shugaba Bola Tinubu don cimma burin ci gaban al’umma.
Fa'idar shigan gwamna Mutfwang jam'iyyar APC
Ƙungiyar ta bayyana cewa jihar Filato ce kaɗai ba a karkashin mulkin APC ba a yankin Arewa ta Tsakiya.
Zazzaga ya ce shiga jam'iyyar APC zai tabbatar da daidaito da burin Gwamnatin Tarayya a karkashin shugaban kasa Tinubu.
Sanarwar ta kuma nuna damuwa kan rikicin PDP, tana mai cewa idan Mutfwang bai fice daga PDP ba, zai iya rasa damarsa a zaben 2027 mai zuwa.
A watan Afirilun 2024, ƙungiyar ta riga ta aika wasikar gayyata ga gwamnan bayan kotun koli ta tabbatar da nasararsa.
Gwamna Caleb ya jajanta da rasuwar Useni
Kun ji cewa tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya, Janar Jeremiah Useni, ya rasu a yau Alhamis, 23 ga Janairu, 2025, bayan fama da jinya mai tsawo.

Kara karanta wannan
'Babban abu na shirin faruwa': Martanin yan Najeriya da Peter Obi ya ziyarci jigon APC a Kano
Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga danginsa, Sojojin Najeriya, Jihar Filato, da kasa baki daya.
Janar Useni ya yi ayyuka masu daraja a rayuwarsa, ciki har da jagoranci, siyasa, da kokarin tabbatar da zaman lafiya musamman a Arewacin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng