Yan Siyasar Kano da ke Kokarin Sulhunta Kwankwaso da Ganduje
Rikicin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Dr. Abdullahi Umar Ganduje, abu ne da ya dade ana nazarin wace irin matsala ce za ta jawo wannan gagarumar baraka tsakanin tsohon ubangida da mataimakinsa.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Wasu na ganin barakar da ta kunno kai tsakanin tsohon gwamna Rabi'u Kwankwaso da Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ta samo asali ne bayan rasuwar mahaifiyar Abdullahi Ganduje.

Source: Facebook
Akwai alamun lamarin ya faru ne tun kafin wannan lokaci, domin ba boyayyen al'amari ba ne a lokacin da Kwankwaso ya ke yabon tsohon dan takarar gwamnan PDP, Salihu Sagir Takai gabanin zaben 2015.
A lokacin da ake sa ran Kwankwaso zai bayyana tsohon mataimakinsa, Ganduje a matsayin dan takarar gwamna a inuwar APC, an ji shi ya bayyana takai da nagartaccen mutum a jam'iyyar da ba ta dace ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu na ganin irin wadannan kalamai na yabon dan takara a jam'iyyar adawa, manuniya ce a kan wata baraka ko rashin goyon bayan Ganduje, sai dai a lokacin babu wanda ya yi karin bayani a kan zargin.

Source: Facebook
Amma yanzu an samu wasu manyan 'yan siyasar Kano da ake ganin karansu ya kai tsaiko, kuma sun fara neman hada gangamin sulhunta tsakanin Kwankwaso da Ganduje, sun hada da;
1. Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan Kano
Murtala Sule Garo, shi ne mutum na farko da aka ji daga cikin kusoshin jam'iyyun da ke Kano ya yi magana a kan muhimmancin sulhunta Kwankwaso da Ganduje a kwanakin nan.

Source: Facebook
Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da jam'iyyarsa ta APC na yi taron karrama tsofaffin 'yan majalisarsu a Kano.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Murtala Sule Garo ya ce:
"Ni ina kira ga tsofaffin gwamnoninmu da su hada kai su yi aiki tare domin burin guda daya na ci gaban Jihar Kano. Hadin gwiwar shugabanninmu na da matukar muhimmanci wajen samar da ci gaban jama'a."
“Idan suna da kishin Jihar Kano a zuciyarsu da gaske, ina rokon su da su hada kai. Ci gaba ba zai samu ba da rabuwar kai. Dole ne shugabannin siyasa su nuna jajircewarsu ga ci gaban jiharmu ta hanyar aiki tare, ba tare da la’akari da banbancin siyasa ba. Hadin kai shi ne tushen ci gaba mai dorewa."
2. Kofa ya nemi a sulhunta Kwankwaso da Ganduje
Kwanaki kadan bayan kalaman Murtala Sule Garo ne aka ji Hon. AbdulMumin Jibrin Kofa na jam'iyyar NNPP ya fito kafar yada labarai ya na neman a gaggauta neman hanyar sulhu tsakanin shugabannin.

Source: Facebook
Duk da Kofa ya na ganin sulhun ba abu ne da zai zo da sauki ba, amma ya ce dole ne jagororin su zubar da makamansu, kuma su gyara mu'amala kamar yadda addinin musulunci ya bayar da umarni.
Hon, Kofa ya kara da cewa;
“Duk da za su iya cigaba da kasancewa a cikin jam’iyyunsu daban-daban, ya kamata su duba kansu a matsayin ’yan’uwa.
3. Kano: Dan Agundi ya goyi bayan sulhu
Jigo a APC, Baffa Babba Dan Agundi shi ma ya gaggauta nuna goyon bayansa ga kiran sulhunta Kwankwaso da Ganduje, saboda a samar da ci gaba mai dorewa a Kano.

Source: Facebook
Daily Post ta ruwaito cewa Dan Agundi ya kuma bayyana takaicin yadda gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi watsi da kudirin da ya gabatar na samar da majalisa da tsofaffin gwamnoni za su rika ganawa.
Ya ce;
"Tabbas, duk wanda ke da kishin ci gaban Kano dole ne ya mara baya ga shawarar Kofa. Muna goyon bayan ka, kuma za mu ba ka dukkan goyon bayan da ya dace don tabbatar da wannan sulhu tsakanin Kwankwaso, Ganduje, Shekarau, da Kabiru Gaya."
"Akwai yiwuwar sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje," Lauya
A wani labarin, kun ji cewa Lauyan APC, Farfesa AbdulKareem Kana, ya zargi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da kokarin kawo nakasu a siyasar Shugaban APC, Abdullahi Ganduje.
Farfesa Kana ya ce amma ganin yadda tsofaffin gwamnonin su ka dade su na aiki da mu'amala tare, akwai yiwuwar a yi sulhu tare da sasanta junansu a siyasance.
Asali: Legit.ng


