Siyasar Kano: Salihu Sagir Takai ba zai fasa neman takarar Gwamna ba

Siyasar Kano: Salihu Sagir Takai ba zai fasa neman takarar Gwamna ba

'Dan takarar Gwamnan Jihar Kano Malam Salihu Takai yana nan a kan bakan sa na samun tikitin Jam'iyyar adawa ta PDP a zaben 2019 duk da Kwankwaso ya nuna wadanda yake so a 2019

Siyasar Kano: Salihu Sagir Takai ba zai fasa neman takarar Gwamna ba
Salihu Sagir Takai bai da shirin janye takarar Gwamna a Kano
Asali: Depositphotos

Salihu Takai zai yi takara duk da tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso ya tsaida mutanen sa da za su nemi kujerar Gwamnan a PDP. Kwankwaso dai ya zabi 'Yan Kwankwasiyya ne su kara da Gwamna mai-ci Abdullahi Ganduje a zaben 2019.

Kwankwaso ya dauko tsofaffin kwamishinonin sa Abba Kabir Yusuf da Ahmad Abdulsalam su fito takarar Gwamna da Mataimakin sa ne a Kano. Duk da haka Malam Salihu Takai ya nuna cewa ba zai fasa shiga zaben fitar da gwani da za ayi a PDP ba.

KU KARANTA: Kwankwaso ya nemi Takai ya janye shirin neman Gwamna

Kwamitin yakin neman zaben Takai ta tabbatar da cewa a shirye 'Dan takarar yake da ya goga da wanda Kwankwaso ya tsaida wajen neman tikitin Jam'iyyar PDP. A karshen makon nan ne aka tantance Takai a matsayin 'Dan takarar Gwamna a Kaduna.

Kwanaki ne dai Uwar Jam'iyya ta rushe Shugabancin PDP a Kano aka nada wani 'Dan Kwankwasiyya a matsayin Shugaban rikon kwarya. Wannan ya sa Shekarau ya koma APC amma irin su Takai su ka bi Kwankwaso su na sa ran samun tikiti.

Salihu Takai tsohon Kwamishi na a Gwamnatin Shekarau wanda ya dade yana neman Gwamna. Takai ya dade a PDP kafin Kwankwaso da jama’ar sa su bar Jam’iyyar APC kwanaki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel