Jigon APC a Yobe Ya Fice daga Jam'iyya, Ya Fadi Dalilansa

Jigon APC a Yobe Ya Fice daga Jam'iyya, Ya Fadi Dalilansa

  • Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Yobe ta samu naƙasu bayan wani babban ƙusa a cikinta ya raba gari da ita
  • Tsohon daraktan wayar da kan matasa na APC a jihar Yobe, Hon. Sa'idu Hassan Jakusko, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar
  • Ya koka kan yadda aka yi watsi da shi ba tare da yi masa sakayya ba kan wahalar da ya sha domin samun nasarar jam'iyyar a jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Tsohon daraktan wayar da kan matasa na jam’iyyar APC a jihar Yobe, Hon. Sa’idu Hassan Jakusko, ya fice daga APC.

Hon. Sa'idu Hassan Jakusko ya fice daga jam'iyyar ne bisa zargin rashin samun kyakkyawar kulawa daga gwamnatin APC a jihar.

Jigo APC ya fice daga jam'iyyar a Yobe
Jigon APC ya fice daga jam'iyyar a Yobe Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Jigon na APC ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar ne bayan gabatar da takardar murabus ga shugaban jam’iyyar na mazaɓarsa, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

APC ta yi martani bayan El Rufa'i ya kwance mata zani a kasuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa jigon APC ya fice daga jam'iyyar?

Ya ƙara da cewa, bayan kasancewa cikin jam’iyyar tun daga 2019, wasu abubuwa da suka faru kwanan nan a APC, musamman a ƙaramar hukumar Jakusko da jihar baki ɗaya, sun ci karo da ɗabi’unsa da ƙa’idojinsa.

Ya koka kan yadda aka ƙi tunawa da shi duk da irin wahalar da ya sha wajen ganin Gwamna Mai Mala Buni ya samu nasara.

"Na rubuta wannan takarda don sanar da murabus ɗina daga jam’iyyar APC a jihar Yobe, wanda zai fara aiki nan take."
"Na kasance mai mutunta dangantakata da jam’iyyar APC da kuma burin ta na kawo cigaba. Duk da haka, dole ne na ɗauki wannan mataki saboda wasu dalilai."
"Na taka muhimmiyar rawa a tawagar yaƙin neman zaɓe inda muka yi aiki tuƙuru, muka yi amfani da lokacinmu, dukiyarmu da ƙarfinmu don tabbatar nasarar Hon. Mai Mala Buni a matsayin gwamnan jihar Yobe."

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

"Duk da irin ƙoƙarinmu da nasarar da muka samu, ban samu wani yabo ko sakamako daga gwamnati cikin shekaru huɗu da suka gabata ba. Duk da haka, na ci gaba da yin hakuri da kuma nuna biyayya ga jam’iyyar."
“Amma, a lokacin babban zaɓen 2023, na fuskanci ƙalubale da dama. Duk da haka, na yi nasarar jagorantar sauya sheƙar kusan mutane 600 daga jam’iyyun siyasa daban-daban, ciki har da PDP, APGA, AC, da LP zuwa APC."

- Hon Sa'idu Hassan Jakusko

Jigon APC ya ce ba a kyauta masa ba

Ya ce, dukkanin masu sauya shekar an gabatar da su ga shugabancin jam’iyyar, ciki har da shugaban APC da wasu manyan jami’ai.

Sai dai, duk da wannan gagarumar gudunmawa, ba a yi wani abu da zai magance matsalolin da ke cikin mazaɓarsa ba.

Ya bayyana godiyarsa kan damar da ya samu ta bayar da gudunmawa ga ci gaban jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Bayan sukar APC, El Rufai ya yi magana kan shirinsa na barin jam'iyyar

Ya kuma nuna godiya ga shugabancin jam’iyyar da sauran mambobin APC a jihar Yobe bisa haɗin kai da goyon bayan da ya samu a tsawon shekaru.

Sanatan PDP ya koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatan da ke wakiltar mazaɓar Delta ta Arewa, Sanata Ned Nwoko ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP.

Sanata Ned Nwoko ya sauya sheƙa APC inda ya nuna cewa ya yi hakan ne saboda rashin goyon da yake samu wajen tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng