Dan Takarar PDP Ya Tayar da Ƙura, Ya Amince Gwamnan APC Ya Yi Tazarce a 2027

Dan Takarar PDP Ya Tayar da Ƙura, Ya Amince Gwamnan APC Ya Yi Tazarce a 2027

  • Dan takarar PDP a zaben 2023 ya goyi bayan tazarcen Gwamna Umar Bago a 2027, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce daga 'yan PDP
  • PDP ta zargi Isah Liman Kantigi da fifita son kansa a kan burin jam’iyyar tare da alwashin daukar matakin ladabtarwa a kansa
  • Rahotanni sun alakanta matakin Kantigi da dangantakar auratayya tsakaninsa da Gwamna Bago, wanda ya kara dagula siyasar Neja

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Alhaji Isah Liman Kantigi, dan takarar gwamnan PDP a zaben jihar Neja, ya goyi bayan tazarcen Gwamna Umar Mohammed Bago na APC a 2027.

Wannan matakin ya jefa siyasar jihar Neja cikin rudani, tare da diga ayar tambaya kan aminci da hadin kai a jam’iyyar PDP.

Alhaji Isa Kantigi ya kare kansa da ya ce PDP ta hakura gwamnan Neja ya yi tazarce a 2027.
Dan takarar PDP ya amince gwamnan Neja ya yi tazarce a 2027, PDP ta dauki mataki. Hoto: @HonBago, @AlhKantigi
Asali: Twitter

Alhaji Kantigi ya bayyana wannan goyon baya yayin wata tattaunawa da manema labarai ta yanar gizo da ya gudanar daga Dubai a daren Litinin, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

"Ku maida Hausa yaren koyarwa a makarantu," Gwamna ya ba gwamnonin Arewa shawara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan takarar PDP ya marawa Bago baya

Ya yaba wa Gwamna Bago a matsayin “shugaba mai hangen nesa” tare da kira ga mambobin PDP da su daina kashe kudi kan takara da shi.

Kantigi ya bayyana goyon bayansa ga tazarcen Gwamna Bago, yana mai cewa ba zai goyi bayan duk wani dan takarar PDP a 2027 ba.

“Na amince da Mohammed Umaru Bago a matsayin dan takararmu na zaben gwamna a 2027,” Kantigi ya fada, yana kira ga PDP da su rungumi wannan gaskiyar.

'Yan PDP sun nuna fushi da matakin Kantigi

Sai dai, 'yan PDP sun nuna fushinsu da wannan mataki, suna kiran hakan da cin amanar jam’iyya da manufofin ta.

Wasu 'yan PDP sun zargi Kantigi da sauya sheka ba bisa sanin kowa ba zuwa APC, inda suka alakanta hakan da kusancinsa da tsohon gwamna Mu’azu Babangida Aliyu.

Rahotanni sun nuna cewa Sanata Zainab Abdulkadir Kure, sananniya a PDP, ta yi tasiri a kan Kantigi saboda dangantakarsu da Gwamna Bago.

Kara karanta wannan

PDP ta gano dalilin faduwarta zaben 2023, ta fadi jihar da take son kwacewa a 2027

Dan takarar jam'iyyar PDP ya karyata jita-jita

Masu sharhi kan siyasa sun ce ƙanwar Kure, Fatima, tana aure da Gwamna Bago, wanda hakan ya sa aka zargi wannan tasiri a sauya shekarar Kantigi.

Kantigi ya musanta waɗannan zarge-zargen, amma ya bayyana cewa ya ki kalubalantar sakamakon zaben gwamnan jihar saboda rashin tabbacin nasara.

Ya ce matakin da ya dauka lokacin zaben 2023 ya samo asali ne daga rahoton sirri da ya nuna cewa ba zai iya yin nasara a kotu ba.

PDP ta shirya ladabtar da Alhaji Kantigi

Shugabannin PDP sun bayyana rashin jin dadinsu da abin da Kantigi ya yi, tare da yin alkawarin daukar mataki kan abin da suka kira cin amanar jam’iyya

Yahaya Ability, mataimakin shugaban PDP na jihar Neja, ya ce matakin Kantigi a 2023 ya rigaya ya janyo tambayoyi kan amincinsa ga jam’iyya.

Ability ya sanar da kafa kwamiti don bincike kan matakin Kantigi, wanda za a fara daga mazabarsa zuwa matakin karamar hukuma.

Kara karanta wannan

Shugaba a APC ya yi zazzafan martani ga El Rufa'i kan hadaka da 'yan adawa

"Wanda ya ci kudina zai mutu" - Isah Kantigi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Dan takarar gwamnan Neja a karkashin jam’iyyar PDP, Isah Liman Kantigi, ya gargaɗi wadanda suka yi masa rashin amana a zaɓen 2023.

Alhaji Isa Kantigi ya bayyana cewa duk wanda ya karɓi kuɗinsa amma ya ƙi zaɓensa, zai fuskanci masifa mai tsanani a rayuwarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.