Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Sokoto Da Neja

All posts
Key Events
Analysis
Exclusive
11 Posts
Sort by
Our live updates have concluded for the day. Catch up on everything you missed below.
Aisha Musa avatar
daga Aisha Musa

Janar Abdulsalami Abubakar ya kada kuri’arsa

Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, ya kada kuri’arsa a garin Minna, babban birnin jihar Neja.

Tsohon shugaban kasa Abdulsalam yana kada kuri'arsa
Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Sokoto Da Neja Hoto: @TheNationNews
Source: Twitter

Aisha Musa avatar
daga Aisha Musa

Dan takarar gwamnan PDP a Sokoto ya nuna karfin gwiwar shi zai yi nasara

Dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Sokoto, Mallam Saidu Umar, ya kada kuri’arsa a rumfar zabe ta 020 Ubandoma, Sabon-titi, Kofar Atiku ta Sokoto.

Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan ya kada kuri'arsa, Mallam Umar ya ce zuwa yanzu zaben na gudana cikin kwanciyar hankali da lumana yankunan jihar.

Ya ce zaben yau ya fi na shugaban kasa da aka yi yan makonni da suka gabata inda ya nuna karfin gwiwar cewa shine zai yi nasara a zaben, rahoton Thisday.

Dan takarar gwamnan PDP a Sokoto yana kada kuri'arsa
Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Sokoto Da Neja Hoto: @THISDAYLIVE
Source: Twitter

Aisha Musa avatar
daga Aisha Musa

Dan takarar gwamnan APC a Neja ya kada kuri'arsa

Dan takarar gwamnan APC a jihar Neja, Muhammad Umar Bago ya isa mazabarsa inda ya kada kuri’arsa a zaben gwamna da na majalisar jiha da ke gudana.

Dan takarar gwamnan APC a Neja yana kada kuri'arsa
Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Sokoto Da Neja Hoto: @HonBago
Source: Twitter

Aisha Musa avatar
daga Aisha Musa

Yadda guragu suka yi tururuwan fitowa zabe a Minna

Yayin da zaben gwamna ke ci gaba da gudana a jihar Neja, kungiyar masu lalurar nakasa sun ce ba za a barsu a baya ba.

An dai ga guragu da dama a wata rumfar zabe da ke garin Minna inda suka fito don sauke hakkinsu na yan kasa.

Guragu a wajen kada kuri'a a garin Minna
Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Sokoto Da Neja Hoto: @vanguardngrnews
Source: Twitter

Aisha Musa avatar
daga Aisha Musa

Tsohon gwamnan Neja ya kada kuri’arsa

Tsohon gwamnan jihar Neja, Muazu Babangida Aliyu, ya kada kuri’arsa a rumfar zabensa da ke unguwar Tunga a Minna, babban birnin jihar.

Babangida Aliyu yana kada kuri'arsa
Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Sokoto Da Neja Hoto: @TheNationNews
Source: Twitter

Aisha Musa avatar
daga Aisha Musa

Rikici ya barke a wata rumfar zabe Karamar Hukumar Sokoto ta Arewa

An samu hatsaniya bayan wasu matasa sun hana jama’a yin zabe a wata rumfa da ke unguwar Dandima, Karamar Hukumar Sokoto ta Arewa.

Aisha Musa avatar
daga Aisha Musa

Zabe a karamar hukumar Kontogora ta jihar Neja

Da misalin karfe 9:50, zabe na gudana a rumfar sakandare ta gwamnati a karamar hukumar Kontagora ta jihar Neja.

Hakazalika na’urar BVAS na tafiya daidaiba tare da kowani tangarda ba.

Aisha Musa avatar
daga Aisha Musa

Yadda wakilin PDP a rumfar zabe ya kada kuri’a a madadin masu zabe a Sokoto

A rumfar zabe ta 008, Gidan Yumfa, jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke karamar hukumar Wamakko ta jihar Sokoto, an gano wakilin PDP a rumfar yana kada kuri’a a madadin masu zabe, kamar yadda Sahara Reporters ta rahoto.

Wakilin PDP yana kada kuri'a a madadin masu zabe
Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Sokoto Da Neja Hoto: @SaharaReporters
Source: Twitter

Aisha Musa avatar
daga Aisha Musa

An fara kada kuri’a a rumfar zabe ta Bakin-Iku a jihar Neja

A yanzu haka, jama’a sun fara kada kuri’a a rumfar zabe ta Bakin-Iku da ke Karamar Hukumar Tafa, a Jihar Neja kamar yadda jaridar Aminiya ta kawo.

Jama'a na kada kuri'arsu a rumfar zabe
Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana a Jihohin Sokoto Da Neja Hoto: @aminiyatrust
Source: Twitter

Aisha Musa avatar
daga Aisha Musa

Ana shirin fara zabe a rumfar zabe ta Lambar Tukera, karamar hukumar Sokoto

Da misalin karfe 8:33 na safe, jami’an INEC sun kammala duk wani tsare-tsare a gudunmar Tureka da ke karamar hukumar Sokoto.

Komai ya kammala tsaf a rumfar zabe ta Lambar Tukera inda ake shirin fara kada kuri’u.

Aisha Musa avatar
daga Aisha Musa

An fara tantance masu zabe a karamar hukumar Sokoto ta kudu

Jama'a sun fara tururuwa zuwa rumfar zabensu a karamar hukumar Sokoto ta kudu.

Tuni jami'an hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) suka fara tantance masu kada kuri'a a yankin bayan masu zaben sun yi dogon layi.