Gawurtattun ‘Yan Siyasa 6 da Suka Bar Adawa, Suka Koma Jam’iyyar APC a Shekarar 2024
- Fitattun ‘ya ‘yan jam’iyyun adawa irinsu PDP da ta yi mulki na shekaru 16 sun koma APC a shekarar nan mai karewa
- Mukhtar Ramalan Yero ya na cikin wadanda jam’iyyar APC ta jawo hankalinsa, shi da jama’ansa sun sauya-sheka
- A shekarar bana ne kuma aka samu manyan ‘yan siyasar Kudancin Najeriya kamar Anyium Pius Anyim sun bar PDP
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Shekarar 2024 ta zo da abubuwa da-dama, a fagen siyasar Najeriya an ga sauye-sauyen sheka a watannin da suka wuce.

Source: Facebook
A bana, akwai kusoshin jam’iyyun hamayya da wasu dalilali suka jawo, a karshe suka sauya sheka zuwa APC mai mulkin Najeriya.
Daily Trust ta dauki lokaci ta tattaro wasu daga cikin ‘yan adawar da suka canza gida:
'Yan adawar da suka shigo APC a 2024
1. Mukhtar Ramalan Yero
Watanni bayan ya sanarwa duniya cewa ya bar jam’iyyar PDP, sai aka ji tsohon gwamnan na Kaduna ya shiga APC mai ci a kasar nan.
Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya zama gwamna tsakanin 2012 da 2015 a PDP a sakamakon rasuwar mai gidansa Patrick Ibrahim Yakowa.
Ramalan wanda ya fito daga Zariya har yanzu bai samu wani mukami a APC ba kuma bai nuna fara nuna sha’awar tsayawa takara a 2023 ba.
2. Anyim Pius Anyim
Anyim Pius Anyim wanda ya nemi tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023 ya na cikin wadanda suka dawo APC.
Bayan kasancewarsa tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Anyim Pius Anyim ya taba kasancewa sakataren gwamnatin tarayya a PDP.
An rahoto yadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karbi fitaccen ‘dan siyasar a APC.
3. Emeka Ihedioha
Rt. Hon. Emeka Ihedioha ya na cikin asarar da PDP ta yi a shekarar nan. The Cable ta rahoto yadda ‘dan siyasar ya jawo sauye-sauyen sheka.
Emeka Ihedioha ya yi gwamna na ‘yan watanni a jihar Imo, daga baya sai kotun koli ta tsige shi, ta ba Sanata Hope Uzodinma da APC nasara.
A sakamakon sabanin da aka samu a PDP, tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilan ya bar jam’iyyar da ya shiga tun kafuwarta a 1998.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: Sojoji sun kashe hatsabibin shugaban ƴan bindiga da yaransa a Katsina
4. Daniel Bwala
Daniel Bwala ya na cikin fitattun ‘yan adawan da aka ji kwatsam sun bar jam’iyyar PDP, sun koma goyon bayan shugaba Bola Tinubu.
Barista Daniel Bwala ya na cikin jagorori a APC, amma sai aka ji ya koma wajen Atiku Abubakar a zabe, daga baya ya yi watsi da PDP.
Ana haka sai aka ji Bayo Onanuga ya sanar da cewa Bwala ya samu mukami a Aso Villa.
5. Sylvanus Nguji Ngele
A shekarar nan jam’iyyar APC ta shirya bikin a garin Abakaliki a jihar Ebonyi domin karbar Sanata Sylvester Ogbaga Ngele da wasu mutanensa.
Sylvester Ogbaga Ngele wanda yana cikin shugabannin PDP na kasa ya yi watsi da jam’iyyar, shi ma ya yi rajista da APC a cikin watan Mayun 2024.
Tsohon Sanatan na Ebonyi ta Kudu ya bar PDP ne saboda sun gagara samun gwamna.
6. Ezenwo Onyewuchi
Wani ‘dan adawa da APC ta yi wuf da shi a yankin Kudu maso gabas shi ne Ezenwo Francis Onyewuchi wanda yanzu haka Sanata ne mai-ci.
Sanata Onyewuchi ya na cikin ‘yan majalisar da suka sauya-sheka daga jam’iyyar LP bayan sun ci moriyar farin jinin Peter Obi a zaben 2023.
Bayan shi irinsu Tochukwu Okere, Donatus Mathew, Bassey Akiba, Iyawu Esosa da Erthiatake Ibori-Suenu, dukkansu sun koma jam’iyyar APC.
'Dan NNPP ya sake komawa APC
Kwanaki bayan ta gama murna, rahoto ya zo cewa jam'iyyar NNPP ta rasa fitaccen dan siyasa a Kano watau Sani Garka Danbatta zuwa APC.
Alhaji Sani Garka ya sauya sheka zuwa APC kwanaki kuma Sanata Barau Jibrin ya karbe shi a birnin tarayya Abuja, ya ce ya bar Kwankwasiya.
Asali: Legit.ng

