Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Janye Daga Takara, Ya Bar Wa Wanda Jam’iyya Ta Zaba

Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Janye Daga Takara, Ya Bar Wa Wanda Jam’iyya Ta Zaba

  • Korarren gwamnan jihar Imo ya ce ya janye daga takarar da ya fito a zaben Nuwamban wannan shekarar ta 2023
  • Wannan ya faru ne bayan da jam’iyyar PDP a jihar ta amince da tsayar da dan takarar yarjejeniya gabanin zaben
  • Rahoto ya bayyana yadda a 2020 aka tsige gwamnan a kan kujerarsa bayan da aka ayyana shi zababben gwamna

Jihar Imo - Tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha ya janye daga jerin ‘yan takarar zaben fidda gwanin gwamna a jam’iyyar PDP a jihar da ke Kudu maso Gabas, Channels Tv ta ruwaito.

A baya, an tantance tare da tace tsohon gwamnan a matsayin daya daga cikin wadanda za su yi takarar zaben fidda gwani gabanin zaben gwamnan jihar na ranar 11 ga watan Nuwamba.

Sai dai, a cikin wata wasikar da ya fitar a ranar 27 ga watan Maris, Ihedioha ya sanar da shugabannin jam’iyyar PDP cewa, ya bayyana amincewarsa da sadaukarwarsa game dan takarar yarjejeniya da PDP ta tsayar.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaɓen Gwamnoni Na 2023: Jerin Zaɓaɓbun Gwamnoni 5 Da Suka Ci Zaɓe Da Ƙuri'u Mafi Ƙaranci

Yadda dan takarar PDP ya janye daga takara
Emeka Ihedioha, dan takarar PDP da ya janye a jihar Imo | Hoto: PDP Official
Asali: Facebook

Yadda aka kori zababben gwamnan PDP a 2020

A watan Janairun 2020, kotun koli a Najeriya ta kori Ihedioha daga kujerar gwamnan jihar Imo bayan watanni kasa da bakwai da hawansa mulki, rahoton Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A hukuncin da alkalan kotun karkashin jagorancin mai shari’a Tanko Muhammadu sun bayyana Hope Uzodinma na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan na ranar 19 ga watan Maris a 2019 a jihar.

Mai daga kara, Uzodinma ya bayyana cewa, shi ne ya samu kuri’u mafi yawa a zaben amma hukumar zabe ta INEC ta ayyana Ihedioha a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Hukuncin da kotun ta yanke

Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun da ta yanke hukuncin ta ce, an zare kuri’un rumfunan zabe 318 a jihar, inda tace dole a hada dasu cikin sakamakon zaben.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Hawaye sun kwaranya, fitaccen dan majalisa a wata jiha ya riga mu gidan gaskiya

Babban kotun ya gamsu da shaidun da wani babban jami’i ya gabatar a gabansa, inda yace kotun kasa ya yi kuskure a hukuncinsa.

Daga baya, Kekere-Ekun ta ayyana Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna tare da kwace takardar shaidar lashe zaben da INEC ta ba dan takarar PDP Ihedioha.

A yau ne aka dakatar da shugaban PDP na kasa, lamarin da ya jawo martani daga tawagar kamfen jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel