Zaben Gwamnoni: Yadda APC Ta Lashe Jihohi 4 cikin 5 a Karkashin Gwamnatin Tinubu

Zaben Gwamnoni: Yadda APC Ta Lashe Jihohi 4 cikin 5 a Karkashin Gwamnatin Tinubu

  • Jam’iyyar APC mai mulki ta samu nasarar lashe jihohi hudu cikin biyar a zaben gwamna da aka gudanar a karkashin gwamnatin Tinubu
  • Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta samu nasara sau daya tal, inda ta lashe jihar Bayelsa, karkashin jagorancin Douye Diri
  • A yayin da ta samu nasara a Edo, Ondo da kuma wasu jihohi biyu a baren zabukan gwamna, APC ta ci gaba da jan zarenta a siyasar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bayan rantsar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga Mayu, 2023, hukumar INEC ta gudanar da zaben gwamna a jihohi biyar.

Rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyar APC ta zama wadda ta yi nasara a zabukan gwamnoni hudu cikin biyar da aka gudanar a karkashin gwamnatin Tinubu ya zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Tana tsaka da shirye shiryen zabe, jam'iyyar APC ta gamu da babbar matsala a Ribas

Rahoto kan jihohi 4 da APC ta lashe a karkashin gwamnatin Bola Tinubu
Okpebholo da Aiyedatiwa sun ci zabensu a karkashin jam’iyyar APC mai mulki a kasa. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Monday Okpebholo, Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Asali: Facebook

INEC na gudanar da baren zabe a jihohi 8

Duk bayan shekaru hudu, Najeriya na gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya, sai kuma na gwamnoni da na majalisun jihohi a lokaci guda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma akwai wasu jihohi da ake gudanar da zabukan gwamnoninsu a lokuta daban da na gama gari, inji rahoton Nigerian Tribune.

Daga cikin jihohin da ake gudanar da zabukansu ba tare da na shugaban kasa ba akwai Bayelsa, Kogi, Anambra, Imo, Osun, Ondo, Edo, da Ekiti.

Me ya jawo ake gudanar da baren zabuka?

A shekarar 1999, Najeriya ta koma kan tafarkin dimokuradiyya, kuma an gudanar da zabe a lokaci guda a dukkanin jihohin tarayyar kasar nan.

‘Yan takara da dama da ba su gamsu da sakamakon zaben ba sun bukaci kotu da ta kwato masu hakkinsu, da cewar su ne suka lashe zaben.

Kara karanta wannan

Zaɓen Ondo: Jerin manyan waɗanda suka yi nasara da waɗanda tafka asara

Kotun sauraren kararrakin zabe ta bukaci a kori gwamnoni da dama, kuma aka sake gudanar da zabe a wasu jihohin da ke da kalubale a sakamakon zabensu.

Rahoton CivicHive ya nuna cewa tun daga lokacin ne jihohin Najeriya takwas suka zama jihohin da ake gudanar da zabensu a lokaci daban da na sauran gwamnoni.

Zabukan jihohi 5 a karkashin Tinubu

A ranar 11 ga Nuwamba, 2023, an gudanar da zaben gwamnoni a jihohin Bayelsa, Imo, da Kogi sannan a shekarar 2024, an gudanar da zabukan jihohin Edo da Ondo.

1. Zaben gwamnan jihar Bayelsa

An fara gudanar da baren zabe a jihar Bayelsa a shekarar 2023. Akalla jam’iyyun siyasa 16 ne suka shiga zaben gwamnan, inda aka samu 'yan takara mata biyu da maza 14.

Manyan ‘yan takaran sun hada da Diri Duoye na PDP, Eradiri Udengmobofa na Labour Party, Timipre Sylva na APC, da Ogege Mercy na APP (mace).

Kara karanta wannan

'Mun gode Tinubu': Ganduje ya taya Aiyedatiwa murna, ya fadi jihohi 2 da za su kwace

An bayyana Diri na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Bayelsa da aka gudanar a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, 2023.

INEC REC a jihar, Obo Effanga, ya bayyana Diri a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya wanke kananan hukumomi shida daga cikin takwas na jihar.

Diri, ya samu kuri’u 175,196 inda ya doke wasu ‘yan takara 15 da suka hada da babban abokin hamayyarsa, Cif Timipre Sylva na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri'u 110,108.

2. Baren zaben gwamna a jihar Kogi

A daya bangaren kuma, jihar Kogi ta samu ‘yan takara 18, maza 17, da mace 1 a kokarin maye gurbin Yahaya Bello, wanda ya yi wa’adi biyu (ya kwashe shekaru 8 yana mulki).

Manyan ‘yan takaran sun hada da Usman Ododo na APC, Dino Melaye na PDP da Murtala Ajaka na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP).

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaben Ondo: Jerin Kananan hukumomi 15 da jam'iyyar APC ta lashe

Sauran sun hada da, Leke Abejide (ADC), Idoko Ilona (APGA), da Suleiman Fatima (ZLP).

INEC ta bayyana Ahmed Ododo a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kogi a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, inda ya samu kuri’u 446, 237.

A cewar jami’in zaben, Johnson Urama, Ododo ya doke abokin hamayyarsa Ajaka na SDP wanda ya samu kuri’u 259,052.

3. Zaben gwamnan jihar Imo

Jam’iyyu 17 ne suka shiga zaben gwamnan jihar Imo sannan Hope Uzodimma, wanda ke kan karagar mulki ya kasance babban dan takara da ke neman tazarce.

Zaben dai ya hada da Odunzeh Ben, dan takarar jam’iyyar NNPP, Achonu Nneji na jam’iyyar LP (PWD), Anyanwu Samuel na jam’iyyar PDP, da Uzodimma na jam’iyyar APC.

Uzodimma, tsohon Sanata mai wakiltar Orlu (Imo ta Yamma) kuma gwamnan jihar mai ci tun 2019, ya lashe zaben gwamnan jihar a 2023.

Kara karanta wannan

APC ta tura ƴan daba sun hargitsa zaben gwamnan jihar Ondo? Jam'iyya ta magantu

IINEC ta sanar da Uzodimma a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan gama fadin sakamakon dukkanin kananan hukumomi 27 na jihar da kuri’u 540,308.

A cewar INEC, dan takarar PDP, Samuel Anyanwu, ya samu kuri'u 71,503 inda ya zo na biyu yayin da dan takarar jam'iyyar Labour, Athan Achonu, ya samu kuri'u 64,081.

4. Baren zaben gwamna a jihar Edo

Baren zabe na farko da aka gudanar a shekarar 2024 ya kunshi 'yan takara 17, wadanda suka hada da maza 16 da mace daya a jihar Edo.

Manyan ‘yan takara a zaben sun hada da Sanata Monday Okpebolo na APC, Asue Ighodalo na PDP, Olumide Akpata na jam’iyyar Labour, da Tom Iseghohi na Action Alliance.

Bayan kammala tattara sakamakon zaben, INEC ta sanar da Monday Okpebolo, dan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Edo a 2024.

Kara karanta wannan

Ondo: An tarwatsa masu zabe da miyagu suka yi ta harbe harbe, an gano dalili

INEC ta sanar a ranar Lahadi 22 ga watan Satumba cewa Okpebolo ya lashe kananan hukumomi 11 cikin 18 na jihar.

A cewar INEC, dan takarar APC ya samu kuri’u 291,667, yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Asue Ighodalo ya zo na biyu da kuri’u 247,274 inda Olumide Akpata na Labour ya samu kuri'u 22,763.

5. Sakamakon Zaben gwamnan Ondo

'Yan takara 17 ne suka fafata a neman kujerar gwamnan jihar Ondo.

Manyan ‘yan takara a zaben sun hada da Lucky Aiyedatiwa na APC, Agboola Ajayi na PDP, Olorunfemi Ayodele na Labour, Akingboye Bamidele na SDP da Abbas Mimiko na ZLP.

A ranar Lahadi, 17 ga Nuwamba, INEC ta sanar da gwamna mai ci Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaben Ondo da aka gudanar a ranar Asabar 19 ga watan Nuwamba.

Farfesa Olayemi Akinwunmi, jami'in tattara sakamakon zaben jihar, ya ce Aiyedatiwa ya lashe kananan hukumomi 18 na jihar da jimillar kuri’u 366,781.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Ondo: Dalilan da za su iya sanya PDP ta lallasa APC a ranar Asabar

Dan takarar da ya zo kusa da Aiyedatiwa shi ne Agboola Ajayi, dan takarar jam’iyyar PDP, wanda ya zo na biyu da kuri’u 117, 845.

"APC za ta kwace Oyo, Osun" - Ganduje

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana jihohin Oyo da Osun a matsayin wadanda jam’iyyar ke shirin kwacewa.

Ganduje buga kirji da cewa APC za ta lashe zaben jihohin Oyo da Osun kamar yadda dan takararta Lucky Orimisan Aiyedatiwa ya lashe zabe a jihar Ondo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.