Ziyarar Yaron Shugaban APC, Ganduje wajen Gwamna Abba Ta Kuma Tado Abin Magana

Ziyarar Yaron Shugaban APC, Ganduje wajen Gwamna Abba Ta Kuma Tado Abin Magana

  • A tsakiyar makon da ya gabata aka ga Abdul'aziz Abdullahi Umar Ganduje tare da Mai girma gwamnan Kano
  • Yaron tsohon gwamnan ya hadu da Abba Kabir Yusuf a lokacin da tawagarsa ta je babban birnin tarayya Abuja
  • Wasu sun ce Malam Abdulaziz Ganduje shi ne babban yaron shugaban na jam’iyyar APC na kasa a duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Abdul'aziz Abdullahi Umar Ganduje ya kuma jawo abin magana wannan karo da aka gan shi tare da gwamnan Kano.

A makon da ya gabata ne Alhaji Abdul'aziz Abdullahi Umar Ganduje ya kai ziyara wajen mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ganduje da Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf da Abdul'aziz Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Abdulaziz Ganduje ya hadu da Gwamna Abba

Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa hoton a shafinsa na Facebook a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Kungiya ta bulla a Kano, ana son Abba ya bijirewa Kwankwaso kafin tafiya tayi nisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Mai magana da yawun bakin gwamnan ya sanar, Abdulaziz Ganduje ya kawowa Alhaji Abba Kabir Yusuf ziyara.

Abdulaziz Ganduje wanda yaron tsohon gwamnan Kano ne ya gana da Abba Kabir Yusuf a gidan gwamnan Kano da ke Abuja.

A hoton da ya rika yawo a shafin Facebook, jama’a sun rika mamaki ganin adawar da ke tsakanin 'yan Kwankwasiyya da Ganduje.

Alakar Abdulaziz Ganduje da Kwankwasiyya

Sai dai ba wannan ne karon farko ba, an taba ganin Abdulaziz Ganduje tare da wasu manyan gwamnati da NNPP a jihar Kano.

Yayin da mahaifinsa yake gwamnan Kano tsakanin 2015 da 2023, Abdulaziz Ganduje ya rika jawo surutu, har da kara gaban EFCC.

Mutane sun yi magana da aka ga Ibrahim Adam ya daura hoton a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Mutane 16 ‘yan gida 1 da suka shiga fagen siyasa kuma suka shahara a Najeriya

Abin da ake fada game da Abdulaziz Ganduje

Wani bawan Allah, Zaharaddeen S Abdullahi ya zarge shi da yin abin da zai batawa Abdullahi Ganduje rai.

Shi kuwa Ahmad Excellency yake cewa ‘Da nagari kenan’

A ra’ayin Taheer Ibrahim Maskawa, akwai bukatar Abba Kabir Yusuf ya nemi wani mukami ya ba yaron tsohon gwamnan na Kano.

Kwamred Umar Waru ya ce:

“Siyasa kenan. Ina tausayawa wand aba ‘dan kowa ba da yake rikici da sunan akida.”

Abba Ganduje yana nan a APC

Ku na da labari cewa Umar Abdullahi Ganduje wanda aka fi sani da Abba, ya na cikin manyan ‘yan jam’iyyar APC a jihar Kano.

Umar Abdullahi Ganduje ya nemi kujerar majalisar wakilan tarayya amma Tijjani Jobe ya yi galaba a kan shi a karkashin APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng