Daga 1991 zuwa 2024: Cikakken Jerin Gwamnonin Soji da Farar Hulan Jihar Edo

Daga 1991 zuwa 2024: Cikakken Jerin Gwamnonin Soji da Farar Hulan Jihar Edo

Edo - A ranar Asabar 21 ga Satumbar 2024 ne masu kada kuri'an Edo za su fito rumfunan zabe tare da yanke shawarar wanda zai jagoranci jihar na shekaru hudu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ko dai 'yan Edo su sake ba jam'iyyar PDP dama a karo na biyu ko kuma su zabi wani dan takarar daga cikin jam'iyyu kusan 16 da suka shiga zaben.

Cikakken sunaye da bayanan gwamnonin da suka mulki Edo daga 1991 zuwa 2024
Bayan mulkin Kanar Yeri a 1991, Edo ta yi wasu gwamnoni 9 ciki har da na farar hula. Hoto: @GovernorObaseki, @adams_oshiomole
Asali: Twitter

Manyan 'yan takara a zaben su ne: Asuerinme Ighodalo na PDP, Sanata Monday Okpebholo na APC da Mista Olumide Akpata na Labour (LP), inji rahoton ThisDay.

Duk dan takarar da aka zaba zai shiga cikin jerin gwamnonin da ba su wuce 12 ba da suka jagoranci jihar tun bayan da ta samu ‘yancin kai a shekarar 1991.

Kara karanta wannan

Girma ya fadi: Basarake ya shiga matsala, ana zarginsa da sace matashi da karbar N2.5m

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga jerin dukkanin gwamnonin da suka mulki jihar Edo da ke Kudu maso Kudancin kasar:

1. Kanar John Ewerekumoh Yeri

Lokacin da aka raba jihar Bendel zuwa jihohin Edo da Delta a 1991, Y. John Ewerekumoh Yeri ya kasance gwamnan soja kuma a fasahance ya zama gwamnan jihar na farko, inji rahoton WikiPedia.

2. John Odigie Oyegun

John Oyegun ne gwamnan farar hula na farko a Edo, wanda aka zabe shi a jam’iyyar SDP a watan Disambar 1991 kuma ya karbi ragamar mulki daga Yeri a watan Janairun 1992.

3. Kanar Mohammed Onuka

Kanal Mohammed Onuka ya gaji Oyegun bayan da sojoji su ka hambarar da farar hula kuma yayi mulki na kasa da shekara guda tsakanin Disamba 1993 zuwa Satumba 1994.

4. Kanar Bassey Asuquo

Asuquo ya rike mukamin gwamnan soji na jihar Edo tsakanin watan Satumba 1994 zuwa Disamba 1996 a lokacin mulkin Janar Sani Abacha.

Kara karanta wannan

Shirin zanga zangar Oktoba: DSS ta cafke ɗan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore

5. Kyaftin Baba Adamu Iyam

Kyaftin Baba Adamu Iyam Iyam ya rike mukamin gwamnan soji na jihar Edo tsakanin watan Agusta 1996 zuwa Agusta 1998. An ce ya kori dubunnan farar hula daga aiki.

6. Kyaftin Anthony Onyearugbulem

Onyearugbulem shi ne gwamnan soji na Edo tsakanin watan Agusta 1998 zuwa Mayu 1999. An ce ya rasu a lokacin da yake neman a zabe shi gwamnan jihar a mulkin dimokuradiyya.

7. Cif Lucky Igbinedion

An zabi Cif Lucky Igbinedion a matsayin gwamnan farar hula na jihar edo a lokacin da mulkin dimokradiyya ya dawo Najeriya a shekarar 1999.

8. Farfesa Oserheimen Osunbor

Farfesa Oserheimen Osunbor ya yi mulki na gajeren wa'adi bayan kotun zabe da ta daukaka kara sun gano cewa akwai kura kurai a zabensa da aka yi tare da tsige shi.

Ya yi gwamna tsakanin Mayu 2007 zuwa Nuwamba 2008.

9. Adams Oshiomhole

Adams Oshiomhole ya hau kujerar gwamnan Edo ne bayan an soke nasarar zaben Osunbor tare da ba shi nasara a shekarar 2008.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Abin da Shettima da Ganduje suka roki al'umma a kamfen zaben jihar

Tsohon shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ya yi wa’adi biyu a Edo har zuwa shekarar 2016.

10. Godwin Obaseki

Godwin Obaseki ya maye gurbin Oshiomhole da cikakken goyon bayansa a shekarar 2016, amma daga baya su biyun suka zamo abokan fadar juna.

Ana saura watanni uku zaben 2020, muka ruwaito cewa Obaseki ya sauya sheka zuwa PDP inda kuma ya samu nasarar yin tazarce karkashin jam'iyyar.

Edo: Dan takarar AA ya janye

A wani labarin, mun ruwaito cewa dan takarar gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar AA, Prince Tom Iseghohi-Okojie ya sanar da ficewa daga zaben.

Prince Tom Iseghohi-Okojie ya kuma sanar da cewa zai goyi bayan dan takarar jam'iyyar APC, Sanata Monday Okpebholo tare da neman magoya bayansa su zabi APC a ranar Asabar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.