Tuna baya: Abubuwa 12 da Oshiomhole ya fadi game da Obaseki a 2016
Hana Gwamna Godwin Obaseki takara da kwamitin tantancewa ta APC tayi bai zo a abun mamaki ga masu lura da siyasar jihar Edo ba.
Idan aka duba abokin adawar Obaseki a siyasa, Kwamared Oshiomhole ne ya karbi rahoton kwamitin tantancewar sa na daukaka kara.
Wannan al'amari ne da ya rufe duk wata kafa da za ta iya bai wa Obaseki damar fitowa takarar kujerar gwamnan a karo na biyu.
Kafin wannan sabani ya shiga tsakanin Oshiomhole da Obaseki a 2016, tsohon shugaban kungiyar kwadagon ya yi yaki sosai don ganin tabbatar tsohon abokinsa a matsayin gwamnan jihar Edo.
A wancan lokacin, Fasto Osagie Ize-Iyamu ya sha kalubale matuka sakamakon zamansa abokin hamayyar Obaseki a jam'iyyar PDP.
KU KARANTA KUMA: Kwanan nan Obaseki zai dawo cikinmu, ba za mu bayar da tikiti kai tsaye ba – Shugaban PDP a Edo
Ga jawabai 12 da Oshiomhole yayi game da Obaseki a 2016:
1. Ubangiji ya san cewa Godwin ya fito ne daga babban gida a masarautar Benin. Ya yi makaranta har matakin jami'a kuma ya fito da sakamako mai daraja.
2. Ya je Amurka inda yayi digirinsa na biyu. Ya dawo ya fara taimakawa jama'a suna kafa kasuwancinsu.
3. Ban damu ba idan Obaseki ya ci amanata daga baya, biyayyar Obaseki ya kamata ta zama ga jama'a ne ba ni ba.
4. Rantsuwar da zai yi don kare kundun tsarin mulkin Najeriya ce kuma zai yi iyakar kokarinsa wurin daga darajar jama'ar Edo. Ba zai yi rantsuwa don wanda ya gada bane.
5. Obaseki ya zama wani bangaren al'adar. Ya san abinda zamu yi da wanda muka sa gaba. Ya san inda muke da abinda zamu shawo kai.
6. Ya yi aiki a kungiyar masana tattalin arziki wacce ya gina ta da abokai a cikin gidan gwamnati ba tare da ya bukaci ko naira daya ba.
7. Na san iyakokina. Ya san nasa. Godwin Obaseki ya yi wa jama'ar jihar Edo aiki na tsawon shekaru bakwai da rabi da kwakwalwarsa ba tare da surutu ba.
8. Mutum kamar Obaseki baya tambayata kwangila. Ya kan ce Kwamared, zamu yi tunanin sannan zamu samu hanyar tabbatar da al'amarin.
9. Jinjina garesa, ku duba jihar Edo, ba mu yi sabbin ayyuka a gidan gwamnati da kudin jihar ba.
10. Ina son a dinga kiran wancan ginin da Godwin Obaseki. Bana ganin Ize-Iyamu a matsayin abokin hamayya.
11. A 2007, ka duba tarihi, Ize-Iyamu buya yake saboda EFCC. Bai yi zabe ba. Ta yaya wanda bai yi zabe ba zai ce shi ya kaini inda nake.
12. Idan za ka dubi takardun makarantar Godwin ka duba na Ize-Iyamu, za ka gane cewa Godwin kwararre ne amma dayan korar shi aka yi daga makaranta a lokacin da yake shekara ta biyu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng