Na yi da na sanin goyon bayan Obaseki a 2016- Oshiomhole

Na yi da na sanin goyon bayan Obaseki a 2016- Oshiomhole

Tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa ya saida wa mutanen jihar gurbataccen kaya a 2016.

Da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar a Oredo Ward 2 a GRA, birnin Benin, tsohon gwamnan ya yi bayanin cewa ya mara wa takarar gwamnan Godwin Obaseki baya a 2016, don tabbatar da ci gaban ayyuka da tsare-tsarensa.

Obaseki ya kasance gwamnan yarjejeniya, amma Fasto Osagie Ize-Iyamu ya kasance bawan Allah wanda zai tabbatar da shugabanci mai inganci a jihar Edo daga ranar 12 ga watan Nuwamban wannan shekarar.

“Na yi kuskure. Allah ne kadai baya kuskure. Shekaruna 68 yanzu. Na zo bayar da hakuri a kan kuskurena na goyon bayan Obaseki a 2016. Na zo jihar Edo domin na gyara kuskurena. Allah na da dalilinsa na abunda ya faru da Ize-Iyamu a 2016. Barin shugabancin APC na kasa domin bani isasshen lokacin gyara kura-kuraina ne.

KU KARANTA KUMA: Musulmai sun koka a kan kisan mummuke da ake masu a hanyar Kudancin Kaduna

Na yi da na sanin goyon bayan Obaseki a 2016 Oshiomhole
Na yi da na sanin goyon bayan Obaseki a 2016 Oshiomhole Hoto: BuzzNigeria.com
Asali: Depositphotos

“Obaseki ya shafe kusan shekaru takwas yana yaudara, yayinda bai aminta da abunda nake yi ba a matsayin gwamnan Edo, amma na mara masa baya, saboda na so ci gaba. Ina mai baku hakuri a kan gurbataccen kaya da na siyarwa da mutanen Edo a 2016. Kowa daga cikinmu na iya wannan kuskuren,” in ji shi.

Ya bayyana cewa a 2007, Ize-Iyamu ya janye masa sannan ya zama darakta janar na kungiyar kamfen dinsa wanda ya yi nasara a dukkanin kananan hukumomi 18 na jihar.

KU KARANTA KUMA: Binciken Magu gagarumin nasara ne, in ji Malami

Zan yi aiki don zaben Ize-Iyamu. Obaseki ya wofantar da amincin mutanen Edo. Da katunan zabenmu, za mu hukunta Obaseki a ranar 19 ga watan Satumba. Ize-Iyamu ba zai maimaita kuskuren Obaseki ba. Ize-Iyamu zai kai jihar Edo zuwa mataki na gaba,” in ji Oshiomhole.

Ya bukaci Ize-Iyamu da ya rike alkawarinsa, inda ya nuna yakinin cewa zai zama mai nasara a zaben ranar 19 ga watan Satumba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel