'Ya Ci Mutuncin Jam'iyya': PDP Ta Dakatar da Tsohon 'Dan Takarar Gwamna a Arewa

'Ya Ci Mutuncin Jam'iyya': PDP Ta Dakatar da Tsohon 'Dan Takarar Gwamna a Arewa

  • Jam'iyyar hamayya ta PDP a Kogi ta dakatar da tsohon dan takarar gwamnanta na zaben 2023 a jihar, Sanata Dino Melaye
  • An rahoto cewa PDP ta dakatar da Melaye ne bisa zargin ya aikata laifuffukan da suka saba da'a da cin mutuncin jam'iyyar
  • Ga dukkan alamu dai kalamansa na baya-bayan nan sun yi illa ga muradu da hadin kan PDP, wanda ya sa aka dakatar da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kogi - Jam’iyyar PDP ta dauki mummunan mataki kan Sanata Dino Melaye, daya daga cikin manyan jiga jigan 'ya'yanta daga jihar Kogi.

An ce PDP ta dakatar da tsohon dan takararta na gwamna a zaben Kogi da ya gabata bisa zargin ya aikata laifuffukan da suka ci mutuncin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Rundunar sojoji ta mika ta'azziyya Borno, za a taimaka wa jama'a

Jam'iyyar PDP ta bayyana dalilin dakatar da Sanata Dino Melaye
Jam'iyyar PDP ta dakatar da Sanata Dino Melaye. Hoto: @_dinomelaye
Asali: Instagram

Jam'iyyar PDP ta dakatar da Dino Melaye

Kwamitin gudanarwar jam’iyyar na gundumar Ayetoro/Iluagba 1 ne ya dauki wannan mataki, a cewar wata takarda da jaridar Tribune ta gani a ranar Juma’a.

Kwamitin jam'iyyar na gundumar ya sanar da dakatarwar ne bayan da ya duba rahoton kwamitin ladabtarwa da aka kafa domin binciken ayyukan Melaye.

Ana zargin Dino da kin amsa gayyatar PDP

SaharaReporters ta rahoto cewa kwamitin binciken ya gayyaci Melaye domin ya amsa tambayoyi kan zarge-zargen da ake yi masa, amma ya ki amsa gayyatar.

Ga dukkan alamu dai kalaman Melaye na baya-bayan nan sun yi illa ga muradu da hadin kan jam’iyyar PDP, wanda ya sa aka dakatar da shi.

Wannan matakin dai ba farau ba ne, domin kuwa jam’iyyar PDP ta dauki irin wannan mataki kan wasu ‘yan jam’iyyar da ta zarga da aikata mata zagon kasa.

Kara karanta wannan

Zaben Kano: Masu neman takara 20 a NNPP sun fadi gwajin kwaya, NDLEA ta magantu

PDP ta dakatar da jiga jiganta

Misali, Peter Babalola, wani jigon PDP daga Osun, an dakatar da shi a watan Agustan 2024 bisa zarginsa da laifin rashin halartar taron jam’iyyar har tsawon shekaru biyu.

A wani bangaren kuma, jam'iyyar PDP ta Benue ta dakatar da tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, bisa zargin ayyukan da suka sabawa jam'iyyar.

Hakazalika, jam’iyyar PDP ta Binuwai ta gayyaci Sanata Gabriel Suswam da wasu 'ya'yanta bisa zargin aikata rashin da'a da kuma cin mutuncin jam'iyyar.

Wadannan matakan sun nuna aniyar PDP na kiyaye da’a da hadin kan jam’iyyar. Sai dai har yanzu babu cikakkun bayanai game da dakatarwar Melaye, amma ana sa ran karin bayani zai biyo baya.

Jam'iyyar PDP za ta hukunta Melaye

Tun da fari, mun ruwaito cewa jam'iyyar PDP reshen jihar Kogi ta bukaci shugabanninta na karamar hukumar Ijumu da su fara shirin dakatar da Dino Melaye.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kadu da ambaliyar ruwa a Maiduguri, ya ba Shettima sabon umarni

Jam'iyyar ta yanke wannan shawarar ne biyo bayan sukar PDP da Dino Melaye ya fito ya yi inda ya shelantawa duniya cewa shugabanninta suka ruguza ta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.