Gwmanan Kano Ya Yi wa Fitaccen Mawakin Siyasa Kyautar Sabuwar Mota, Ya Saki Bidiyo

Gwmanan Kano Ya Yi wa Fitaccen Mawakin Siyasa Kyautar Sabuwar Mota, Ya Saki Bidiyo

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya gwangwaje daya daga cikin mawakan da suka yi masa hidima a lokacin yakin zabe
  • Mawakin da aka sani da Shalelen Mawaka, ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa ya samu kyautar sabuwar mota daga gwamnan
  • Mutane sun yi dafifi a kasan hoto da bidiyon motar da mawakin ya wallafa, inda su ke yiwa Gwamna Abba godiya kan karamcinsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yiwa Shalelen Mawaka, daya daga cikin fitattun mawakan Kwankwasiya kyautar sabuwar mota.

Shalelen Mawaka na daya daga cikin wadanda suka ba da gagarumar gudunmowa a lokacin yakin neman zaben Gwamna Abba Yusuf a Kano.

Kara karanta wannan

TSA: Abba ya sa a rufe dukkanin asusun bankin hukumomi da ma’aikatun Kano

Mawakin siyasa ya samu kyautar sabuwar mota daga gwamnan Kano
Shalelen Mawaka ya wallafa hoto da bidiyon motar da Gwamna Abba Yusuf ya ba shi kyauta. Hoto: shalelenmawaka
Asali: Instagram

Abba ya ba mawaki kyautar mota

A cikin wata sanarwa mai dauke da hoto da kuma bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Shalelen Mawaka ya nuna motar da gwamnan ya ba shi kyauta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce kudin motar, wadda ta ke kirar Peugeot 406 ta haura Naira miliyan hudu, abin da wasu ke ganin mawakin ya canci wannan babbar kyauta.

Shalelen Mawaka ya wallafa cewa:

"Abba Gida Gida ne ya ce Shalele kaima ga wannan sabuwar motar kafin sauran alherai. Mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf Allah ya saka da alheri."

Mutane sun taya Shalale murna

Legit Hausa ta tattaro ra'ayoyin wasu daga cikin mabiyan mawakin kan wannan kyautar mota da ya samu daga gwamnan Kano.

Basheer Abubakar Abdullahi:

"Masha Allah. Allah ya sanya alkhairi. Indai anyi hakuri hakika kam kowa zai samu."

Kara karanta wannan

Kano: Majalisa ta nemi taimakon Gwamna Abba bayan iftila'in da ya faru a jihar

Basheer Hamza Gwammaja:

Masha Allah, Allah Ubangiji ya sanya alkhairi. Shi kuma mai girma gwamna Allah ya saka masa da alkhairi."

Shehu Amiru:

"Tabbas an yi abin da ya dace, kuma hakuri ya na da rana, na tabbata ba iya wannan motar ce alkhairi a tsakaninku da Gwamna Abba Kabir Yusuf ba, da sauran abubuwa nan gaba."

Muhammad Usman Inuwa:

Masha Allah. Ubangiji ya kara rufa asiri duniya da lahira, sai munzo dani."

Abba Mustapha Inuwa:

"Alhamdulillah. Ina taya ka murna."

Duba bidiyon motar a nan kasa:

Rarara ya ba da kyautar mota

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen mawakin siyasar Arewa da ma kasa baki daya, Dauda Kahutu Rarara ya yiwa Abubakar Bashir Maishadda kyautar sabuwar mota.

An ce Dauda Rarara ya gwangwaje furodusa Maishadda da sabuwar motar kirar Mercedes-Benz, mai launin fari kan irin kokarin da ya ke a shirya bidiyoyin wakokinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.