Hotuna: Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya gwangwaje Bashir Maishadda da sabuwar mota
A ranar Lahadi, mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara ya gwangwaje furodusa Abubakar Bashir Maishadda da sabuwar mota, kirar Mercedes-Benz, mai launin fari.
Furudusan, ya bayyana hakan a shafinsa na Instagram @realabmaishadda, inda ya ke yiwa Allah godiya tare da godewa mawakin kan wannan babbar kyauta da ya yi masa.
Abubakar Maishadda, ya wallafa cewa: "Alhamdulillah. Alhaji Dauda Adamu Rarara @@real_dauda_kahutu_rarara, Ina Godiya. Allah ya biyaka da Gidan Aljannah CHAIRMAN"
KARANTA WANNAN: 'Yadda muka kashe wasu masu jego, kuma muka yi awon gaba da jariransu'
Kusan gaba daya jaruman shirya fina finan Hausa, da sauran ma'aikatan masa'antar sun taya furodusa Maishadda murnar samun wannan kyauta daga mawakin.
Abubakar Bashir Maishadda, shine ya dauki kambun girma na masu shirya fina finan Hausa a Kannywood, sakamakon manyan fina finan da ya shirya.
Wannan kyautar tana zuwa ne, a lokacin da mawaki Dauda Rarara ke daukar bidiyon wakokin da ya yi a 'yan kwanakin nan, wadanda tuni suka fara karade kasar.
KARANTA WANNAN: Fargabar kawo hari: An tsaurara matakan tsaro a Abuja da kewaye
Akwai wakar da ya yi mai taken "Kasata ce", wacce ya zayyana halin da kasar Nigeria ta ke ciki, musamman ma Arewa, na matsalar tsaro da tabarbarewar tattalin arziki.
Mawakin ya nuna yadda shugaba Buhari ya nada 'yan Arewa sama da 87 a manyan mukamai, amma hakan bai haifar da wani ci gaba a yankin na Arewa ba.
A wata wakar kuma, ya nuna murnarsa na komawar tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Yakubu Dogara jam'iyyar APC, inda ya yi mata taken "Dogara ya dawo".
A cikin ma'aikatan daukar wannan bidiyon, jarumi kuma mai bayar da umurni a fina finan Hausa, Ali Nuhu, shi ne ya ke bayar da umurnin bidiyon wakokin.
Abubakar Bashir Maishadda ne ya ke shirya bidiyon.
Ana daukar bidiyon wakokin ne a jihar Katsina, tare da wasu manyan jarumai na masana'antar Kannywood, da suka hada da masu barkwanci da kuma 'yan rawa.
KARANTA WANNAN: Buhari zai kaddamar da shirin tallafawa 'yan kasuwa da N50,000 a kowanne wata
Idan ba a manta ba, Dauda Kahutu Rarara ya ba shugaban kamfanin jaridar Kannywood Exclusive, Isah Bawa Doro, kyautar mota kirar Peugeot 206 launin bula.
A wani labarin; Rundunar 'yan sanda ta cafke wasu gawurtattun masu safarar yara a jihar Rivers, wadanda suka labarta yadda suka kashe wata mai jego tare da awon gaba da jaririnta.
Bayan sace jaririn, kungiyar masu safarar, sun labarta yadda suka sayar da shi, da kuma raba kudin a tsakanin, kafin dubun su ta cika, aka cafke su.
Masu safarar, Mary Ishamel (68) tare da abokin aikinta, Chinedu Nwachukwu (23), na daga cikin mutane 15 da rundunar 'yan sandan jihar Rivers ta yi holensu ga manema labarai.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng