Ya Haura Miliyan 20: Sanata Kawu Sumaila Ya Fadi Albashin da Ya Ke Karba duk Wata

Ya Haura Miliyan 20: Sanata Kawu Sumaila Ya Fadi Albashin da Ya Ke Karba duk Wata

  • Dan majalisar dattawa daga mazabar Kano ta Kudu, Sanata Kawu Sumaila ya ce ana biyansa kimanin N600,000 matsayin albashi a duk wata
  • Sai dai Sanata Kawu Sumaila ya ce yana karbar Naira miliyan 21 matsayin kudin gudanarwa a duk wata, wanda ke tashi Naira miliyan 22
  • Bayanin sanatan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tababa kan hakikanin albashi da alawus din 'yan majalisar tarayya ke karba a duk wata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Har yanzu dai ana kan tababa kan yawan albashi da alawus din 'yan majalisar tarayya ke karba yayin da Sanata Kawu Sumaila ya fito ya fadi kudin da ake ba shi duk wata.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka wakana a taron Tinubu da tsofaffin shugabannin Najeriya a Aso Rock

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ne ya fara fallasa albashin sanatocin kasar, inda har ya zargi 'yan majalisar tarayya da kayyade albashinsu.

Sanata Kawu Sumaila ya yi magana kan albashin da ya ke karba duk wata
Sanata Kawu Sumaila ya ce albashi da alawus da ya ke karba duk wata ya kai N22m. Hoto: @MohmmedMasud
Asali: Twitter

A rahoton BBC Hausa, Kawu Sumaila, wanda sanata ne mai wakiltar Kano ta Kudu daga jam'iyyar NNPP ya bayyana cewa yana karbar Naira miliyan 21 ne duk wata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Albashin sanatoci a tsarin hukumar RMAFC

Dan majalisar dattawan ya ce albashi da alawus da hukumar tattara haraji da kula da kasafi (RMAFC) ce ke da alhakin kayyade albashi da alawus na masu rike da mukaman siyasa.

"Albashin da na ke karba a wata bai kai Naira miliyan 1 ba. Idan aka cire haraji da sauransu, kudin na dawowa N600,000 ko sama da hakan da kadan."

- A cewar dan majalisar dattawan.

Sanata Kawu Sumaila ya ce bai kamata albashin 'yan majalisar tarayya ya zama wani abin da za a ci gaba da yin ce-ce-ku-ce a kansa ba, saboda ba wani yawa ne da shi ba.

Kara karanta wannan

Matatar man Dangote za ta sayar da litar fetur a kan N600? Kamfanin ya yi karin haske

Sanatan Kano ya fadi albashinsa a wata

Sai dai kuma Sanata Kawu Sumaila ya bayyana cewa yana karbar Naira miliyan 21 a duk wata matsayin kudin gudanarwa, baya ga kayyadadden albashinsa daga RMAFC.

Dan majalisar dattawan na jam'iyyar NNPP ya ce saboda karin da aka samu, kowane sanata yanzu yana tashi da Naira miliyan 22, da suka hada da albashi da alawus, inji Leadership.

Amma sanatan ya ce bai san hakikanin kudin da aka halatta a ba shi a matsayinsa na sanata ba, inda ya ce Naira miliyan 22 da ya ke karba da su ya ke gudanar da dukkanin ayyukansa.

Game da kudin da shugabannin majalisar dattawa ke karba, Sanata Kawu Sumaila ya ce bai san abin da ake biyansu ba.

RMAFC ta fadi albashin sanatocin Najeriya

Tun da fari, mun ruwaito cewa hukumar tattara haraji da kasafin kudi (RMAFC) ta bayyana cewa kowane sanata daga cikin sanatoci 109 na karbar albashi da alawus na N1,063,860 a duk wata.

Kara karanta wannan

Ana cikin surutu, gwamnati ta jero kuɗin da ake turawa kowane sanata duk wata

Shugaban RMAFC, M. B. Shehu, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya ce ikirarin Sanata Shehu Sani na cewa ana biyan sanatoci N13.5m matsayin kudin gudanarwa ba gaskiya ba ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.