Albashin Sanatocin Najeriya a kowane wata - Bincike

Albashin Sanatocin Najeriya a kowane wata - Bincike

A yayin da mafi akasarin al'ummar Najeriya ke ci gaba da kafa kahon zuka wajen neman masaniya ta albashi da kuma alheran da Sanatocin Najeriya ke samu a kowane watan duniya, a yau Legit.ng ta kawo muku wannan bukata cikin rahusa.

Walkiyar da ta haskawa al'ummar Najeriya ainihin albashin Sanatocin Najeriya a shekarar 2018 da ta gabata ta bayar da tabbacin cewa, kowane Sanata na daukar albashi na Naira 700,000 kacal a kowane wata.

Sai dai wannan adadi na kudi bai hadar da alheran da Sanatocin ke ribata ba sakamakon gudunmuwa da tsayuwar daka wajen taka rawar gani yayin sauke nauyi al'ummomin da suke wakilta a fadin Najeriya.

Albashin Sanatocin Najeriya a kowane wata - Bincike

Albashin Sanatocin Najeriya a kowane wata - Bincike
Source: Depositphotos

Baya ga wannan tumuni na zunzurutun albashi, gwamnatin Najeriya na kuma bayar da alheri na Naira 13,500,000 da misalta a matsayin alawus ga Sanatocin a kowane wata. Ba bu shakka wannan alheri ya ninku sau bila adadin idan an kwatanta da albashin su na kowane wata.

Hasken wannan walkiya ya fadada ne yayin da wakilin shiyyar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani, ya farkewa abokanan aikin sa Laya ta hanyar zayyanawa al'ummar Najeriya irin makudan kudi da suke samu a kujerar su.

Yayin da masana ilimin lissafi na da ta su ranar, sun bayyana cewa, kowane Sanata na Najeriya na samun kimanin Naira miliyan 14 a kowane wata, inda a shekara zai tara dukumar dukiya ta Naira miliyan 170,400,000.

KARANTA KUMA: Yakin Neman Zabe: Jami'an tsaro sun shirya tarbar Buhari a jihar Kano

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, Sanatocin Najeriya na samun alawus mai girman gaske domin share masu hawaye da dauke nauyin da ke kan su musamman wajen sayen jarida, gyaran Mota, biyan kudaden wayar salula da hawa yanar gizo, gyaran gida, kula dalafiya da sauran su.

Rahotanni sun bayyana cewa, an yi itifakin Sanatocin Najeriya 109 sun yiwa takwarorin su na sauran kasashen fintinkau ta fuskar samun albashi da kuma alheran kujerar su mafi tsoka da girman gaske.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel