Manyan Abubuwan Magana 10 da Suka Faru a Majalisar Tarayya Daga 2023 Zuwa 2024
Daga lokacin da aka rantsar da majalisar tarayya ta goma, abubuwa da-dama sun faru a cikin shekara guda kenan.
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Sanata Godswill Akpabio da Rt. Hon. Tajuddeen Abbas su ke rike da shugabancin majalisar dattawa da wakilai.
Abubuwan da suka faru a Majalisa
Daily Trust ta dauko manyan abubuwan da suka jawo surutu a majalisar daga lokacin da aka rantsar da ita a Yunin 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Sabon taken Najeriya
A gurguje ‘yan majalisar tarayya suka amince da sabon taken Najeriya wanda ya sa aka rabu da Arise O Compatriots zuwa We Hail Thee.
2. Motocin ‘yan majalisa
Legit ta kawo maku rahotannin yadda gwamnatin Najeriya ta kashe fiye da N50bn domin sayawa ‘yan majalisa motocin hawa kirar SUV.
3. Wa’adin shugaban kasa
Wasu ‘yan majalisa 35 sun kawo kudirin da zai ba shugaban kasa dama yin wa’adi guda rak na tsawon shekaru shida a kan karagar mulki.
4. Komawa mulkin Firayim Minista
Hon. Abdulsamad Dasuki da wasu abokan aikinsa sun kawo shawarar a komawa salon shugabancin Firayim Minista da aka bari a 1966.
5. Binance da zargin 'yan majalisa da rashawa
Kwanaki New York Times ta rahoto shugaban kamfanin Binance, Richard Teng yana cewa ‘yan majalisa sun nemi cin hanci a hannunsu.
6. Kudirin hana gantalin dabbobi
Sanata Titus Tartenger Zam ya kawo kudirin da zai ba da damar kafa wurin kiwon dabbobi, hakan zai hana makiyaya gantali a jihohi.
7. Aikawa ‘yan majalisa kudi
Ana shirin tafiya hutu ne aka ji Godswill Akpabio ya yi subutar baki, ya shaidawa ‘yan majalisa an aiko masu kudin da za su shakata.
8. Binciken badakalar daukar aiki
Kwamitin Hon. Yusuf Adamu Gagdi ya binciki zargin badakala wajen daukar aiki a hukumomi da ma’aikatu, wannan ya jawo yamutsi.
9. Zargin badakalar N3.7tr a kasafin kudi
Sanata Abdul Ningi ya yi zargin cewa akwai N3.7tr da ke cikin kasafin kudi da ba a ware su ga wasu kwangiloli ba, hakan ya tada kura.
10. Dakatar da Abdul Ningi
A dalilin fitowa yana zargin badakala a kasafin kudin shekarar 2024, majalisar dattawa ta dakatar da Abdul Ningi na tsawon watanni uku.
Yadda majalisa ta yaki tazarcen Obasanjo
Ana da labarin cewa tsohon shugaban majalisar dattawa ya tona yadda aka so ba shi cin hanci domin tazarcen Olusegun Obasanjo.
Sanata Adolphus Wabara ya bayyana adadin kudin da aka tura masa har gida domin yarda kudirin a lokacin, amma ya ki yarda.
Asali: Legit.ng