Kano: NNPP Ta Gano Makarkashiyar APC Domin Hana Mulkin Gwamna Abba Samun Nasara
- Yayin da ake cikin rigimar sarautar Kano, jam'iyyar NNPP ta bayyana waɗanda ke neman ruguza jihar Kano a Arewacin Najeriya
- Jam'iyyar ta zargi APC da neman kawo rudani a jihar domin kwace mulkin jihar karfi da yaji kuma ta kowace hanya
- Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin Gwamnatin Tarayya da shiga rigimar jihar wajen amfani da bangaren shari'ar da jami'an tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Jam'iyyar NNPP a Najeriya ta zargi APC da neman kawo rudani a jihar Kano.
Jam'iyyar ta zargi APC mai mulki da neman kwace mulkin Abba Kabir a jihar Kano ta kowace hanya wajen kawo rudani.
NNPP ta zargi APC a rigimar Kano
Wannan na kunshe ne a cikin hirar da kakakin jam'iyyar ta kasa, Ladipo Johnson ya yi da Plus TV a ranar Laraba 19 ga watan Yunin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Johnson ya ce APC na neman kifar da gwamnatin Abba Kabir Yusuf karfi da yaji wajen kawo rudani a jihar, cewar Vanguard.
Ya ce yadda APC ta yi kane-kane a rigimar sarautar Kano hakan ya nuna damuwarta wurin kwace mulkin Kano ta kowace hanya.
"APC ba su taba boye maitarsu ta neman rikita Kano da kwace ikon halastaccen Gwamna Abba Kabir ba."
- Ladipo Johnson
NNPP ta shawarci ƴan Najeriya kan APC
Jami'yyar NNPP ta ce APC na amfani da bangaren shari'a da kuma jami'an tsaro domin kawo rudani a jihar.
Ta bukaci ƴan Najeriya da su tashi tsaye kan wannan makirci da APC ke ƙullawa da ba zai haifar da ɗa mai ido ba.
Kwankwaso ya zargi Tinubu kan rigimar Kano
A wani labarin mai kama da wannan, Sanata Rabiu Kwankwaso ya zargi Gwamnatin Tarayya kan rigimar sarautar Kano.
Kwankwaso ya ce Bola Tinubu yana kokarin kawo rudani a jihar domin sanya dokar ta ɓaci da kwace mulkin Kano.
Daga bisani, Bola Tinubu ya musanta zargin da Kwankwaso ya ke yi kan gwamnatinsa inda ya ce babu kamshin gaskiya a maganar.
Asali: Legit.ng