Tsagin NNPP Ya Ƙaryata Kwankwaso, Ya Faɗi Masu Yunkurin Tayar da Hargitsi a Kano

Tsagin NNPP Ya Ƙaryata Kwankwaso, Ya Faɗi Masu Yunkurin Tayar da Hargitsi a Kano

  • Tsagin jam'iyyar NNPP karkashin jagorancin Boniface Aniebonam ya nesanta kansa da kalaman Rabiu Kwankwaso kan rigimar sarautar Kano
  • Da yake zantawa da manema labarai a Legas, Aniebonam ya ce NNPP ba ta da alaƙa da zargin gwamnatin tarayya ke rura wutar rikicin Kano
  • Ya jaddada cewa tsagin NNPP ya kori Kwankwaso tuntuni saboda haka ba ruwan jam'iyyar da kalaman da ya yi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Tsagin Dokta Boniface Aniebonam a NNPP, ya nesanta jam'iyyar da kalaman Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya yiwa jam'iyyar takara a 2023.

Boniface ya ce jam'iyyar NNPP ba ta da alaƙa da zargin da Kwankwaso ya yi cewa gwamnatin tarayya ce take rura wutar rikicin sarautar da ke faruwa a Kano.

Kara karanta wannan

Kano: Bidiyon buldoza ya ja hankalin mutane yayin da Abba ke shirin rusa Fadar Aminu

Rabiu Kwankwaso.
Tsagin Aniebonam a NNPP ya nesanta kansa daga ikirarin da Kwankwaso ya yi Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Ya yi wannan furucin ne yayin zantawa da manema labarai a Legas kan danbarwar Kano, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan za ku iya tunawa Kwankwaso ya yi zargin cewa jami'an tsaron da ke da alhakin tabbatar da zaman lafiya, sun fake da umarnin kotu suna kare Sarki na 15, Aminu Ado Bayero.

Haka nan kuma Kwankwaso ya zargi gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Tinubu da APC mai mulki da yunƙurin kirkiro sabuwar kungiyar Boko Haram ta zamani.

Tsagin NNPP ya musanta kalaman Kwankwaso

Da yake martani kan ikirarin Kwankwaso, Mista Aniebonam ya ce tsagin NNPP da yake jagoranta ba ya tare da waɗannan zarge-zarge.

A cewarsa, matsayar jam'iyyar NNPP ta ƙasa game da rigimar sarautar Kano ita ce lamari ne da ya shafi siyasar cikin gida a jihar Kano, rahoton Within Nigeria.

Kara karanta wannan

Kano: NNPP tayi martani, ta ce APC na yunƙurin ƙwace mulki daga Gwamna Abba

Ya ƙara da cewa irin wannan zargi mai nauyi mara tushe da aka ɗorawa gwamnatin tarayya abin Allah-wadai ne domin yana iya tayar da hargitsi a jihar.

'Kalaman Kwankwaso ka iya tada hargitsi'

"Mun jima da korar Kwankwaso daga tsagin jam'iyyarmu, saboda haka duk kalaman da ya faɗa ba shi da alaƙa da NNPP ta ɓangaren mu."
"Muna da yakinin cewa Gwamnatin Tarayya za ta iya shiga tsakani ta sasanta lamarin idan har ta fahimci za a kai ga asarar rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano.
"Amma irin wannan zargi ba tare da hujja ba, ba ya cikin aƙidarmu, kuma daidai yake da tsokano rigima wanda bamu yarda da haka ba,"

- Boniface Aniebonam.

Wani jigon NNPP kuma ɗan Kwankwasiyya ya shaida mana cewa babu wani Jagora sai Kwankwaso a jam'iyya mai kayan marmari.

Malam Sa'id ya faɗawa wakilin Legit Hausa cewa tsagin da ke ikirarin sun kori Kwankwaso ba ƴan NNPP bane domin ba su san me suke yi ba.

Kara karanta wannan

Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu ya saduda, ya nemi ayi sulhu da gwamnati

"Waɗannan ƴan Legas ɗin ba su san me ake ciki a NNPP ba, burinsu kawai su taɓa Kwankwaso, idan ka duba duk abin da ke faruwa a ƙasar nan ba su ce komai ba sai da Mai gida ya yi magana."
"Saboda haka ni ban ɗauke su ƴan jam'iyya ba, na san dai tunda kaji Kwankwaso ya zargin Gwamnatin Tinubu to tabbas akwai wani abu a ƙasa, duba da Ganduje na da ƙarfi a sama," In ji shi.

Kotu ta bayyana halastaccen Sarkin Kano

A wani rahoton kuma Babbar kotun tarayya ta yanke hukunci kan dambarwar masarautar Kano tun bayan rushe masarautun jihar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.

Mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman a hukuncin da ya zartar a yau ya soke dokar da ta rushe masarautun Kano, sannan ya yi umarnin kowa ya tsaya a matsayinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262