Tsohon Gwamnan Sokoto Ya Bayyana Illar Siyasar Uban Gida, Ya Shawarci Gwamnatoci

Tsohon Gwamnan Sokoto Ya Bayyana Illar Siyasar Uban Gida, Ya Shawarci Gwamnatoci

  • Sanata Aliyu Wamakko ya yi magana kan siyasar uban gida da ake yi a Najeriya inda ya bayyana matsayarsa kan haka
  • Wamakko ya ce bai yarda da tsarin sukar gwamnatocin da suka shude ba saboda ba shi ne tsari mai kyau ba
  • Tsohon gwamnan Sokoto daga bisani ya ba gwamnatoci shawara kan yadda za su inganta harkokin noma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Tsohon Gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayyana yadda ya ke gidanar da rayuwarsa bayan barin mulki.

Wamakko ya ce shi a tsarinsa ba ya zargi ko sukar shugabannin da suka bar mulki saboda ba shi ne abin da ya kamata ba.

Kara karanta wannan

"Kalamanka ba su dace da shugaba ba," Peter Obi ya caccaki Tinubu kan talauci a Najeriya

Tsohon gwamnan Sokoto ya yi magana kan siyasar uban gida
Tsohon Gwamnan Sokoto, Aliyu Wamakko ya magantu kan illar siyasar uban gida. Hoto: Aliyu Magatakarda Wamakko.
Asali: Facebook

Wamakko ya fadi illar siyasar uban gida

Sanatan ya bayyana haka ne a hirarsa da BBC Hausa inda ya yi magana kan lamarin siyasar uban gida a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Akwai siyasar uban gida da ke da haɗari da ake yi a wasu wuraren da ba muradin jama’a ake kulawa ba."
"Amma yana da kyau a inda ake fifita ra’ayin jama’a fiye da son kai a siyasa."

- Sanata Aliyu Wamakko

Sanata Wamakko ya kawo hanyar inganta noma

Tsohon gwamnan ya tabo harkar noma inda ya bayyana hanyoyin samun nasara ga kowace gwamnati da ya shafi bangaren noma.

Ya ce samar da tallafin kudi domin jama'a su yi noma shi ne kawai zai samar da kayan abinci a cikin kasa tare da rage kudin taki.

“Babu yadda za a yi nasara a noma idan aka ce ana raba buhun taki daya ga manomi ko kwano biyu."

Kara karanta wannan

Sarkin Kano: Kotu ta soke nadin da aka yiwa Sanusi II? Ga karin haske kan hukuncin

“Yaya za a yi da wannan? Wannan ba za a kira shi da tallafi ba, wasa ne ake yi da noma, ka ga an ba karamar hukuma motar taki biyu."

- Sanata Aliyu Wamakko

Kwankwaso ya magantu kan matsalar Arewa

Kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana babbar matsalar Arewacin Najeriya musamman wanda a shafi rashin tsaro.

Sanatan ya ce rashin iya shugabanci a kasar shi ne musabbabin rugujewar yankin wanda ya yi silar rashin tsaro.

Kwankwaso ya koka kan yadda 'yan siyasa suke amfani da kudi da kayayaki wurin yaudarar masu zabe a kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.