Bayan Farmakin Matasa, Ɗan Majalisar Tarayya Ya Tsorata, Ya Yi Abin Alheri a Mazaɓarsa

Bayan Farmakin Matasa, Ɗan Majalisar Tarayya Ya Tsorata, Ya Yi Abin Alheri a Mazaɓarsa

  • Ɗan Majalisar Tarayya a jihar Osun, Soji Adetunji ya gwangwaje ƴan mazaɓarsa da abin alheri domin inganta rayuwarsu
  • Adetunji ya raba kekunan dinki da babura da injunan markade da talabijin domin jama'a su dogara da kansu a mazabarsa
  • Wannan na zuwa ne bayan farmakin da matasan yankin suka yi kan ɗan Majalisar kan zargin rashin katabus

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun - Kwanaki hudu kacal bayan farmaki da matasa suka kai masa a jihar Osun, ɗan Majalisar Tarayya ya yi rabo a mazabarsa.

Dan Majalisar da ke wakiltar Ifelodun/Boripe da Boluwaduro, Soji Adetunji ya raba talabijin da kekunan dinki da babura.

Kara karanta wannan

Kotun koli ta tanadi hukunci a shari'ar da Tinubu yake yi da Gwamnoni 36

Dan Majalisar Tarayya ya yi rabo bayan harin da matasa suka kai masa
Dan Majalisar Tarayya a jihar Osun ya gwangwaje ƴan mazabarsa.
Asali: Original

Ɗan Majalisa ya raba kaya a mazabarsa

Adetunji ya dauki matakin ne bayan farmaki da matasa suka kai masa kan zargin rashin tabuka wani abu ga ƴan mazaɓarsa, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasan sun kai masa harin ne a ranar Asabar 8 ga watan Yuni yayin bikin aure a Ada da ke jihar.

Hadimin ɗan Majalisar a bangaren yada labarai, Nurudeen Abolaji ya bayyana cewa matasan yankunan Ikirun da Iragbiji da Agba ne suka kai harin.

Duk da harin da aka kai masa, Adetunji ya raba kayayyakin a makarantar Akirun inda ya ce ya yi hakan ne domin kyautatawa al'ummarsa.

Dan Majalisa ya fadi musabbabin raba kayan

"Na yi hakan ne domin samarwa jama'a abin da za su dogara da kansu inda kowa zai ci gaba."
"Samar da wadannan kaya zai inganta kasuwanci da kirkira-kirkire a mazaɓata."

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rigimar sarautar Kano, gwamna ya take Sultan, zai sauya dokar masarautu

- Soji Adetunji

Wasu daga cikin al'ummar yankin sun yabawa Adetunji kan wannan kokari da ya yi na rabon kayan tallafi.

Dan Majalisa ya raba raguna a Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa ɗan Majalisar Tarayya da ke wakilate mazabar Kaura Namoda/ Birnin Magaji, Hon. Aminu Jaji ya gwangwaje ƴan mazaɓarsa.

Jaji ya raba raguna guda 300 da kuma kudi har N250m domin gudanar da bukukuwan sallah cikin lumana.

Kyautar za ta shafa shugabannin jam'iyyar APC da mambobinta da kuma mata da matasa da sauran marasa karfi a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.