Girma Ya Kare: Fitaccen Ɗan Siyasa Ya Shiga Masifa Bayan Daure Shi Shekaru 4 a Gidan Kaso

Girma Ya Kare: Fitaccen Ɗan Siyasa Ya Shiga Masifa Bayan Daure Shi Shekaru 4 a Gidan Kaso

  • Dubun ɗan siyasa ta cika bayan daure shi da kotu ta yi shekaru hudu a gidan gyaran hali kan zargin kona tafkekiyar gona
  • Mista Tajudden Babatunde wanda tsohon shugaban karamar hukuma ne a jihar Osun ya amince da aikata laifukan
  • Kotun ta kuma hada da wasu mutane shida da ake zargi da hadin baki da cin amana yayin hukuncin da ta gabatar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun - Kotun Majistare da ke birnin Osogbo a jihar Osun ta daure tsohon shugaban karamar hukuma shekaru hudu a gidan yari.

Kotun ta dauki matakin ne kan Mista Tajudden Babatunde wanda ya shugabanci karamar hukumar Iwo ta Yamma a jihar Osun.

Kara karanta wannan

Ana daf da gudanar da zabe, 'yan bindiga sun harbe jigon dan takarar PDP

Dan siyasa ya sha daurin shekaru 4 a gidan kaso
Kotu ta daure tsohon shugaban karamar hukuma shekaru 4 a gidan yari a jihar Osun.
Asali: Original

Mene ake zargin dan siyasar a Osun?

An daure Babatunde ne a ranar Alhamis 6 ga watan Yuni kan zargin hadin baki da barna sa kuma cinna wuta a wata ƙatuwar gona, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran wadanda aka yanke musu hukuncin tara sun hada da Sunday da Ajoko da Jonas John da Kohonu Deboye da Adeoye Alabi da kuma Kasumu Ajao.

Duka mutane shidan da ake zargi sun tabbatar da laifukansu kafin yanke musu wannan hukunci a kotun, cewar Daily Post.

Matakin da alkalin kotu ya ɗauka

Alkalin kotun, Mai Shari'a A. Famuyide ya ba Ajao zabin tarar N80,000 saboda shekarunsa da kuma rashin lafiya.

Ana zarginsu da shiga wata gona inda suka yanke bishiyoyin kwakwar manja kusan guda 400 da kudinsu ya N10m.

Daga bisani bayan tafka barna da suka yi a gonar sai suka cinnawa mata wuta suka tsare abinsu.

Kara karanta wannan

"Jima'i kadai ke rage mana kunci": 'Yan gudun hijira sun cika sansani da jarirai

Yan bindiga sun harbe dan takarar PDP

A wani labarin, kun ji cewa 'yan bindiga sun bindige wani dan takarar shugabancin karamar hukuma a jam’iyyar PDP a jihar Enugu.

Marigayin mai suna Ejike Ugwueze ya gamu da ajalinsa ne yayin da ya ke tuki kan hanyar Neke Odenigbo a karamar hukumar Enugu ta Gabas.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Juma’a 7 ga watan Yuni a yankin inda maharan suka zagaye shi tare da bindige shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel