Clark Ya Fallasa Yadda Jonathan Suka Ƙaƙaba Wike Ya Zama Gwamnan Rivers a 2015

Clark Ya Fallasa Yadda Jonathan Suka Ƙaƙaba Wike Ya Zama Gwamnan Rivers a 2015

  • Ɗaya daga dattijan kudu maso kudu a kasar nan, Edwin Clark ya gargaɗi tsohon sanata George Sekibo da ya gyara kalamansa kan rikicin jihar Rivers da ake yi a yanzu
  • Dattijon ya bayyana cewa mutanen ƙabilar Ijaw ne su ka cicciɓa Nyesom Wike zuwa matakin siyasar da ya taka a yau saboda haka babu dalilin ba shi haƙuri a halin da ake ciki ba
  • Edwin Clark ya bayyana cewa a lokacin da wa'adin mulkin Rotimi Amaechi ya zo ƙarshe, ɗan ƙabilar Ijaw ne ya kamata ya yi gwamna , sai tsohon shugaba Jonathan ya roƙa masa alfarma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Abuja- Ɗaya daga shugabannin shiyyar kudu maso kudancin ƙasar nan, Edwin Clark ya bayyana yadda tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan da mai ɗakinsa, Patience Jonathan su ka ƙaƙaba musu Nyesom Wike a matsayin gwamna. Mista Clark ya ce bayan wa'adin Rotimi Amaechi ya kara a 2015, tsohon shugaban da matarsa suka roƙi masu ruwa da tsaki da a ba Wike dama duk da lokaci ne na ɗan ƙabilar Ijaw ya yi gwamna.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya fadi abu 1 da ba zai daina yi ba a Najeriya

Edwin Clark, Goodluck Jonathan, Nyesom Wike
Jigo a kudu maso kudu, Edwin Clark ya ce tsohon shugaba Jonathan ne ya roki alfarma su ka zaɓi Wike a Rivers Hoto: Edwin Clark, Goodluck Jonathan, Nyesom Wike
Asali: Facebook

Vanguard News ta wallafa cewa Edwin Clark ya ce ƴan ƙabilar Ijaw ne su ka taka rawa wajen ɗaukakar Nyesom Wike a jihar Rivers.

Clark ya yi gargaɗi kan siyasar Rivers

This day ta wallafa cewa dattijon na kudu maso kudu, Edwin Clark ya gargaɗi tsohon Sanata, George Sekibo kan kalamansa dangane da siyasar jihar Rivers.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana takun saƙa tsakanin gwamnan Rivers mai ci Siminalayi Fubara da tsohon gwamna Nyesom Wike.

A buɗaɗɗiyar wasikar da Edwin Clark ya aikawa Sanata Sekibo, ya ce mutanen ƙabilar Ijaw ne su ka cicciɓa Wike zuwa matakin da ya ke na siyasa a yanzu.

Dattijon ya ƙara da cewa bai ga dalilin da zai sa a ba Nyesom Wike haƙuri ba tun da babu laifin da aka yi masa.

Wike ya umarci a durkusawa Tinubu

Kara karanta wannan

Ana cikin halin kunci a Najeriya jigon PDP ya fadi abin da ya kamata a yiwa Tinubu

Mun kawo labarin cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana dalilansa na ba manyan sakatarorin gwamnatin umarnin su fito su durkusawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Bayaninsa ya biyo bayan cece-kuce tsakanin ƴan Najeriya bayan an gano shi ya bawa sakatarorin unarnin su yiwa Tinubu durƙusawar girmamawa saboda karamcin da ya yi musu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.