Tambuwal Ya Fadi Dalilin da Ya Sa 'Yan Najeriya Suka Tsinci Kansu Cikin Tsadar Rayuwa

Tambuwal Ya Fadi Dalilin da Ya Sa 'Yan Najeriya Suka Tsinci Kansu Cikin Tsadar Rayuwa

  • Aminu Waziri Tambuwal ya yi magana kan halin ƙuncin da ƴan Najswriya suka tsinci kansu a cikin a halin yanzu
  • Tsohon gwamnan na jihar Sokoto ya bayyana cewa ƴan Najeriya sun yi babban kuskure ta hanyar sake miƙa ragamar ƙasar nan a hannun jam'iyyar APC
  • Tambuwal ya buƙaci ƴan adawa da su haɗa ƙarfi da yaji domin ganin sun kawar da jam'iyyar APC daga madafun ikon ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya ɗora alhakin halin ƙuncin da ƴan Najeriya suke ciki kan sake zaɓen jam'iyyar APC da suka yi a zaɓen 2023.

Sanatan mai wakiltar Sokoto ta Kudu, ya bayyana cewa ƴan Najeriya sun yi babban kuskure sake dawo da APC kan karagar mulki.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fusata, ya ba da sabon umarni kan kisan da aka yiwa sojoji a Abia

Tambuwal ya magantu kan halin tsadar rayuwa a Najeriya
Tambuwal ya ce 'yan Najeriya sun yi kuskure sake zaben APC a 2023 Hoto: Aminu Waziri Tambuwal
Asali: Facebook

Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana hakan ne a yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a Sokoto ranar Lahadi, 2 ga watan Yunin 2024, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane kuskure Tambuwal ya ce ƴan Najeriya sun yi?

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa sun gargaɗi ƴan Najeriya kan sake zaɓen jam'iyyar APC amma suka yi kunnen uwar shegu da jan kunnen da aka yi musu.

"A lokacin yaƙin neman zaɓe a 2023, mun gargadi ƴan Najeriya da kada su sake yin kuskuren zaɓen APC a mulki domin ba su da wani abin kirki da za su iya yi."
"Mun ce musu APC ba ta shirya shugabancin ƙasar nan ba. Abin da suke so shi ne su ƙwace mulki su gan su a cikin ofisoshi."
"Yanzu sun ƙwace iko kuma sun shiga ofis amma ba su san abin da za su yi da shi ba."

Kara karanta wannan

Matawalle ya dauki zafi kan kisan sojoji a Abia, ya fadi matakin dauka

"Kuma yanzu ƴan Najeriya sun samu kansu cikin halin ƙunci saboda gazawarsu."

- Aminu Waziri Tambuwal

Tambuwal ya shawarci ƴan adawa

Sai dai tsohon gwamnan ya yi kira ga ƴan adawa da su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tabbatar da cewa jam’iyyar APC ta sha kaye a zaɓe mai zuwa, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

"Haƙƙi ne a kanmu mu haɗa kai domin tabbatar da cewa APC ta yi rashin nasara a a dukkanin matakan gwamnati."

- Tambuwal

Ya yabawa shugabannin jam’iyyar bisa yadda suka haɗa kan jam’iyyar wanda hakan ya sanya ƙarfinta ya ƙaru.

Tambuwal ya gurfana gaban kwamiti

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya gurfana a gaban kwamitin shari'a na jihar da aka kafa domin binciken wasu almundahana da ake zarginsa da aikatawa a lokacin mulkinsa.

Aminu Tambuwal wanda ke wakiltar Sokoto ta Kudu a majalisar dattawa ya isa ofishin kwamitin binciken ne tare da wasu muƙarrabansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel