Tsohon Gwamnan Sokoto Ya Gurfana Gaban Kwamitin Shari’a, Ana Zargin Ya Tafka Almundahana

Tsohon Gwamnan Sokoto Ya Gurfana Gaban Kwamitin Shari’a, Ana Zargin Ya Tafka Almundahana

  • Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya gurfana gaban wani kwamitin shari'a don amsa tambayoyi kan zargin almundahana
  • Gwamnan jihar na yanzu, Ahmad Aliyu ne ya kafa kwamitin don bincikar kadarori da Tambuwal ya karkatar a lokacin da ya ke gwamna
  • Tambuwal ya bayyana cewa, ya gurfana gaban kwamitin ne don kara tabbatar wa 'yan Najeriya cewa babu wanda ya fi karfin shari'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

A ranar Asabar ne tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya gurfana a gaban kwamitin shari'a na jihar da aka kafa domin binciken wasu almundahana da ake zarginsa da aikatawa a lokacin mulkinsa.

Mista Tambuwal wanda ke wakiltar Sokoto ta Kudu a majalisar dattawa ya isa ofishin kwamitin binciken ne tare da wasu mukarrabansa.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnonin PDP sun nemi Tinubu ya yi murabus, sun fadi dalili

Gwamnatin Sokoto na tuhumar Aminu Waziri Tambuwal da ayyukan almundahana.
Gwamnatin Sokoto na tuhumar Aminu Waziri Tambuwal da ayyukan almundahana. Hoto: @AWTambuwal
Asali: Twitter

Gwamnatin Sokoto ta kafa kwamitin binciken Tambuwal

Sai dai bai samu damar ba da shaida a gaban kwamitin ba saboda dage zaman da aka yi tare da cewar za a sanar da shi ranar zama na gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A watan Yulin 2023, gwamnan jihar, Ahmed Aliyu, ya kafa wani kwamitin bincike na mutum biyar, don bincikar duk wani fili ko kadarorin gwamnati da gwamnatin Tambuwal ta sayar.

Kafa kwamitin binciken yana bin ikon da aka baiwa gwamna a sashe na 1(2) na kwamitin binciken, a dokokin Cap. 33 na jihar Sokoto na shekarar 1996, Daily Nigerian ta ruwaito.

Abin da Tambuwal ya ce bayan zuwansa ofishin kwamitin

Amma Mista Tambuwal, wanda ya tabbatar da zuwansa ofishin kwamitin a shafin sa na X, ya ce:

“Da safiyar yau ne na gurfana a gaban mai shari’a Mu’azu Abdulkadir Pindiga a karkashin kwamitin binciken shari’a na jihar Sokoto wanda magajina Ahmad Aliyu ya kafa.

Kara karanta wannan

Kano: An yi korafi yayin da Abba Kabir ya ware N5.32bn don abinci da gyararraki a gidan gwamnati

“Na samu rakiyar tawaga ta lauyoyi da wasu jami’an gwamnatina da suka hada da tsohon SSG, Muhammad Mainasara Ahmad, tsohon shugaban ma’aikata, Muktar Magori, tsohon babban lauyan gwamnati, Dr. Sulaiman Usman, SAN."

Tambuwal ya kara da cewa:

“A yayin jagorantar matasa, dole ne mu cusa musu akidar mutunta doka da kuma hukumomin da aka kafa. Ayyukan hidimtawa jama’a da muka yi za su fanshe mu a koyaushe.
“A matsayinmu na ’yan kasa, ya kamata mu gane cewa, babu wani mutum, ko mai girman matsayin sa ya ke sama da dokokin kasa, musamman ma kundin tsarin mulkin Najeriya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel