Shekara 1 a Mulki: 'Dan PDP Ya Bayyana Sunayen Gwamnoni 3 Mafi Taka Rawar Gani

Shekara 1 a Mulki: 'Dan PDP Ya Bayyana Sunayen Gwamnoni 3 Mafi Taka Rawar Gani

  • Jigo a jam’iyyar PDP, Rilwan Olanrewaju ya yabawa Ademola Adeleke na Osun, Ahmadu Fintiri na Adamawa, da Sheriff Oborevwori na Delta
  • Rilwan Olanrewaju ya bayyana cewa wadannan su ne gwamnonin da suka ciri tuta wajen iya aiki a watanni 12 da suka gabata
  • Jigon PDP ya zabi gwamnonin uku ne bisa kokarinsu a inganta ababen more rayuwa, da tabbatar da zaman lafiya a jihohin su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jigo a jam’iyyar PDP, Rilwan Olanrewaju, ya bayyana sunayen gwamnoni uku da suka taka rawar gani a cikin shekara guda da suka yi a kan karagar mulki.

Jigon PDP ya yi magana kan gwamnonin da suka fi tabuka abin kirki a jihohinsu
Jerin gwamnonin da suka taka rawar gani a Najeriya. Hoto: @GovernorAUF, @AAdeleke_01, @RtHonSheriff
Asali: Twitter

Ayyukan gwamnoni a shekara 1

A cewar Olanrewaju, Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun da takwarorinsa na jihohin Delta da Adamawa, Sheriff Oborevwori da Ahmadu Fintiri, su ne suka fi yin aiki a Najeriya a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Sarki 2 a lokaci 1: Lauyoyin Kano sun fitar da jawabi ganin an jibge jami'an Sojoji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon na PDP ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da jaridar Legit.ng.

Rilwan Olanrewaju, ya bayyana cewa gwamnonin suna yin iya kokarinsu wajen ganin sun samar da shugabanci na gari ga al’ummarsu.

An yabawa Adeleke, Fintiri da Oborevwori

'Dan siyasar ya kuma yabawa gwamnonin kan aiwatar da manufofi da ke daukar hankali, inganta ababen more rayuwa, da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihohinsu.

Sai dai ya lura cewa gwamnonin na yin abin da za su iya yi ne kawai domin shugaban kasa da ministoci ne galibi ke aiwatar da tsare-tsaren kasa.

A cewar jigon na PDP:

“Ina yin kira ga sauran gwamnonin da su jajirce wajen kawo sauyi a jihohinsu ta yadda ‘yan kasa za su ci gajiyar dimokuradiyyar da ta dora su a mulkin."

Kara karanta wannan

Yan sanda sun yi biyayya ga kotu, 'har yanzu aminu ado bayero ne sarkin Kano'

Gwamnatin tarayya ta yi karar gwamnoni

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta shigar da kara a gaban Kotun Koli a kan rashin da’a da gwamnonin jihohin kasar nan 36 ke yi a ayyukan kananan hukumomi.

Karar da babban lauyan tarayya (AGF) kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi ya shigar, na neman cikakken ‘yancin cin gashin kai ga daukacin kananan hukumomin kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel