Sanusi II vs Ganduje: Tsofaffin Gwamnoni da Suka Fadi Zaɓe Bayan Faɗa da Sarakuna

Sanusi II vs Ganduje: Tsofaffin Gwamnoni da Suka Fadi Zaɓe Bayan Faɗa da Sarakuna

A ranar Alhamis 23 ga watan Mayu, Gwamna Abba Kabir ya dawo da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 16.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Wannan mataki ya biyo bayan tube sarkin da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta yi a ranar 9 ga watan Maris din shekarar 2020.

Ganduje da tsofaffin gwamnoni da suka yi fada da sarakuna
Sanusi II vs Ganduje: Jerin tsofaffin gwamnoni da suka fadi zabe bayan faɗa da sarakunan. Hoto: @masarautarkano, @OfficialAPCNg.
Asali: Twitter

Ganduje ya kirkiro masarautu guda hudu bayan na Kano wanda ya yi amfani da hakan wurin tube Sanusi II daga mulki.

Legit ta tattaro wasu tsofaffin gwamnoni da suka samu matsala da manyan sarakunan jihohinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: Ganduje vs Sanusi II

Ana tunanin tube Muhammadu Sanusi II daga karagar mulki na daga cikin dalilan da ya saka Ganduje rasa mulkin Kano a hannunsa.

Kara karanta wannan

Sarki 2 a lokaci 1: Lauyoyin Kano sun fitar da jawabi ganin an jibge jami'an Sojoji

Ganduje ya zargi Sanusi II da goyon bayan Sanata Rabiu Kwankwaso na NNPP wanda a zaben 2023 suka lallasa Ganduje da jami'yyar APC.

Oyo: Alao Akala vs Oba Lamidi

Marigayin tsohon gwamnan Oyo, Otunba Alao Akala ya fara takun-saka da Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi bayan hawa karagar mulki.

Tun farko, Akala ya samu goyon bayan Alaafin a farkon hawa mulkinsa kafin komai ya rikice bayan gwamnan ya naɗa wani sarki ba tare da sanin Alaafin ba.

Alaka ta kara tsami bayan basaraken ya ki amsa gayyatar sulhu da gwamnan da shugaban kasa a wancan lokaci, Olusegun Obasanjo ya kira, cewar Vanguard.

Daga bisani Akala ya rasa yin nasara a zaben 2011 bayan rasa kananan hukumomi hudu a jihar.

Osun: Oyetola vs Oba Jimoh

Tsohon gwamnan Osun, Gboyega Oyetola kuma ministan albarkatun ruwa shi ma ya rasa komawa kujerarsa bayan takun-saka da basarake lamba daya a jiharsa.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya bayyana rawar da Tinubu ya taka wajen dawo da shi kan sarautar Kano

Matsalar ta fara ne bayan Ataoja na Osogbo, Oba Jimoh Oyetunji ya gargadi kada a hana dan takarar PDP, Ademola Adeleke wanda yanzu shi ne gwamnan jihar shigowa fadarsa.

Basaraken ya ce gwamnatin PDP ce ta daura shi a sarauta inda ya ce zai fi yi mata biyayya madadin jam'iyya mai mulki ta APC.

Bayan rashin nasara a zaben jihar, an yi zargin Oyetola yana kokarin tube basaraken daga karagar mulki.

Abba ya rusa masarautun Kano 5

Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir ya rusa masarautun Kano guda biyar bayan sanya hannu a dokar Majalisar jihar.

Daga bisani Abba Kabir ya mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano na 16 a ranar Alhamis 23 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.