Tube rawanin Sanusi: Dattijan Kano sun yi wa Ganduje zazzafan martani

Tube rawanin Sanusi: Dattijan Kano sun yi wa Ganduje zazzafan martani

Kungiyar dattijan jihar Kano ta kalubalanci sauke Sanusi Lamido a matsayin sarkin Kano da Gwamnan Abdullahi Ganduje yayi. Sun kuma yi alkawarin daukar mataki a kan abinda gwamnatin jihar tayi.

Idan zamu tuna, gwamnan ya fitar da takarda a ranar Litinin ta hannun sakataren gwamnatinsa, Usman Alhaji, a kan tube rawanin sarki Muhammadu Sanusi II a kan abinda ya kwatanta da rashin da’a ga tanadin dokokin masarautun jihar Kano.

Kamar yadda sakataren gwamnatin jihar ya bayyana, sarkin baya halartar taron majalisar sarakunan jihar Kano da kuma sauran tarukan da gwamnati ke shirya wa, kuma ba tare da bayar da wani dalili ba.

A takardar da shugaban majalisar dattijan Kano, Bashir Usman Tofa yasa hannu, ya kwatanta tube rawanin Sarkin da abin takaici kuma wanda aka yi ba tare da bin ka’ida ba.

Shugaban ya kara da kira ga jama’ar jihar da su kwantar da hankalinsu ba tare da an tada husuma ko hatsaniya ba.

Tube rawanin Sanusi: Dattjan Kano sun yi wa Ganduje zazzafan martani
Tube rawanin Sanusi: Dattjan Kano sun yi wa Ganduje zazzafan martani
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Shehu Sani ya yi 'jirwaye' a kan tube rawanin Sarki Sanusi II

Mu dattijan Kano mun fada tsananin damuwa da fargabar takardar da sakataren gwamnatin jihar kano ya karanta mai bayyana tube rawanin Mai martaba, Muhammadu Sanusi II a matsayin gwamnan jjihar Kano.

“A sakamakon wannan abun alhinin da Gwamnan Ganduje yayi, muna kira ga Kanaawa da su kwantar da hankulansu don hargitsi ba zai samar da mafita ba.

“Mun yarda da ikon Allah kuma zamu ci gaba da amincewa da duk abinda ya kaddara. Shi ke da mulki,” takardar ta ce.

“Duk da haka, za mu kalubalanci wannan lamarin ta halastacciyar hanya. A takaice dai zamu bibiyi shari’armu da ke kalubalantar majalisar jihar Kano din karkashin Gwamnan wacce ta tumbuke sarkin,” cewar takardar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel