"Da Wahala", Jigon APC Ya Gaji da Kame Kamen Tinubu Wajen Gyara Najeriya Kamar Lagos

"Da Wahala", Jigon APC Ya Gaji da Kame Kamen Tinubu Wajen Gyara Najeriya Kamar Lagos

  • Yayin da ƴan Najeriya ke kokawa kan matsalolin kasar, jigon APC ya nuna damuwa kan yadda ake gudanar da mulki
  • Salihu Lukman ya bayyana damuwa kan salon mulkin Shugaban Bola Tinubu inda ya ce zai yi wahala a samu nasara
  • Lukman ya yi kokwanto kan yadda Tinubu ya yi alkawarin gyara Najeriya kamar Lagos inda ya ce ba a kama hanya ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban APC a yankin Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya sake caccakar Shugaba Bola Tinubu.

Lukman ya ce alamu sun ƙara tabbata cewa Tinubu ba zai iya gyara Najeriya ba kamar yadda ya yi a Lagos.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Kwanaki bayan samun mukami, tsohon Gwamna ya kare Tinubu

Jigon APC ta sake caccakar salon mulkin Tinubu
Jigon APC, Salihu Lukman ya koka kan salon mulkin Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Salihu Lukman.
Asali: Facebook

Lukman ya koka da mulkin Tinubu, APC

Jigon APC ya ce a yanzu kullum Tinubu saka shakku ya ke yi a zukatan mutane madadin kara musu karfin guiwa, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya koka kan yadda gwamnatin Tinubu ta ke ci gaba da kuntatawa ƴan Najeriya madadin rage wahalar da ake ciki, Daily Post ta tattaro.

"Abin takaici, Tinubu madadin ya cire yan kasar a kunci sai sake jefa su cikin wasu matsaloli ya ke yi da kuma koma baya."
"A dalilin haka, rashin tsaro ya samu gindin zama ga talauci da rashin aikin yi da kuma uwa uba hauhawan farashin kaya."

- Salihu Lukman

Jigon APC ya zargi shugabanni da sakaci

Lukman ya ce abin takaici ne duk da shafe shekaru 25 a dimukradiyya, ba a samu shugabanni da ke da burin bunkasa ƴan kasar da cire su a halin da suke ciki ba.

Kara karanta wannan

Lauyoyin Murja sun yi fatali da ita, sun fadi nadamar da suka yi a shari'arta

Ya koka kan yadda aka ja wadanda suka yaki Tinubu a zaben 2023 a jiki bayan ya dare kujerar shugaban kasa.

An zargi Ganduje da ruruta rikicin Rivers

Kun ji cewa, Tsohon Minista a Najeriya, Edwin Clark ya zargi shugabannin APC da PDP da kara hura wutar rikicin jihar Rivers.

Clark ya ce Abdullahi Ganduje da kuma Umar Damagun na PDP sun ba da gudunmawa sosai wurin kara rikicin siyasar jihar.

Ya buƙace su da su tsame hannunsu a cikin matsalar jihar da ke samar da mafi yawan kaso na tattalin arzikin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel