Gwamna Fubara Ya Fadi Ainihin Lokacin da Ya Fara Mulkin Jihar Rivers

Gwamna Fubara Ya Fadi Ainihin Lokacin da Ya Fara Mulkin Jihar Rivers

  • Gwamna Siminalayi Fubara ya fito ya bayyana lokacin da ya fara mulkin jihar Rivers wacce ke da ɗumbin arziƙin man fetur
  • Gwamnan ya bayyana cewa ya fara mulki a watan Fabrairun 2024 ne wanda hakan ke nufin watanni huɗu da suka gabata
  • Kalaman gwamnan na zuwa ne yayin da yake ci gaba da takun saƙa da magabacinsa kuma ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya ce ya fara mulki na gaske ne watanni huɗu da suka gabata.

Hakan na nufin a watan Fabrairun 2024 ba lokacin da aka rantsar da shi a matsayin gwamna ba a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan ya tsoma baki kan rigimar Ministan Tinubu da gwamnan PDP

Fubara ya magantu kan mulkin Rivers
Gwamna Fubara ya ce ya fara mulki ne a watan Fabrairun 2024 Hoto: @SimFubaraKSC
Asali: Twitter

Kalaman na Fubara ba za su rasa nasaba da rikicin siyasar da yake yi da magabacinsa kuma ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ba wanda ya fara tun daga shekarar da ta gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa gwamnan ya bayyana hakan ne a wurin ƙaddamar da aikin wata hanya.

Yaushe gwamna Fubara ya fara mulki?

"Yanzu muka fara, amma ina ba ku tabbacin cewa za ku ƙara samun kulawa. Idan har a cikin watanni hudu za mu iya yin hakan, sannan mu samu yabo, za a sha mamaki a nan gaba."
"Nan da shekara ɗaya zuwa shekara biyu a gwamnatinmu, jihar Rivers za ta ga mulki saɓanin wanda ta saba gani a baya."
"Na san dalilin da ya sanya na ce watanni huɗu. Mun fara cikakken mulki ne a watan Fabrairun 2024. A wannan lokacin ne muka fara yanke hukunci sannan muka fara tunkarar mulki."

Kara karanta wannan

"Mu taimaka masu," Ganduje ya yi magana kan mummunan harin da aka kai Masallaci a Kano

"Ina alfahari da cewa mutanenmu suna farin ciki da abin da muka gudanar."

- Siminalayi Fubara

Alwashin Gwamna Fubara ga 'yan Rivers

Gwamna Fubara, ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan da za su amfani al'ummar jihar.

Ya kuma bayyana cewa baya yin rufa-rufa kan ayyukan da yake gudanarwa inda ya yi nuni da cewa dukkanin bayanan ayyukan da ya yi suna nan, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Batun rikicin siyasar Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan ya buƙaci a sasanta rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar Rivers domin dawo da zaman lafiya.

Jonathan ya kuma roƙi Gwamna Siminalayi Fubara da ministan Abuja, Nyesom Wike su kawo ƙarshen wannan lamari kuma su haɗa kai su yi aiki tare.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel