Tattaunawar Hadakar Atiku Abubakar da Peter Obi Ta Fara Daukar Hankalin APC

Tattaunawar Hadakar Atiku Abubakar da Peter Obi Ta Fara Daukar Hankalin APC

  • Da alamu hankalin APC y afara karkata kan yadda dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ke tattaunawa da takwaransa na LP, Peter Obi
  • Ana ganin shugabannin biyu na saka labule domin tattaro dabarun kwace mulkin kasar nan daga hannun shugaba Bola Ahmed Tinubu a kakar zaben 2027
  • Sai dai jami’in hulda da jama’a na APC, Felix Morka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata ya bayyana kokarin hadakar da motsi ne kawai wanda ya fi labewa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Hankalin jam’iyyar mai mulki ta APC ya fara karkata kan tattaunawar hadakar da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, da takwaransa na LP, Peter Obi.

Kara karanta wannan

Shugaban makaranta ya tsere da kudin jarrabawar WAEC da NECO, ya lula kasar waje

A ‘yan kwakin nan, jiga-jigan biyu sun gana da juna a wani batu da ake yi wa lallon daura damarar tunkarar zaben 2027.

Atiku Abubakar
Alamun hadakar Atiku Abubakar da Peter Obi ya fara daukar hankalin APC Hoto: Atiku Abubakar, Mr Peter Obi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Nigerian Tribune ta tattaro cewa tuni tsohon shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa sun samu fahimtar juna, kuma akwai kwakkwarar alama da ke nuna cewa za a tafi tare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin APC kan hadakar Atiku,Obi

Da alama tattaunawar Atiku Abubakar da Peter Obi ya fara daukar hankalin APC mai mulki da ita ce ake yi wa kujerar da ta rike barazana.

A wata sanarwar da sakataren yada labaran APC, Felix Morka ya fitar a ranar Talata, ya bayyana hadakar da wani abu mai kama da motsi ya fi labewa, kamar yadda The Cable ta wallafa.

Ya kara da cewa ‘yan siyasar biyu na kokarin hadewa ne kawai saboda tsabar takaicin da ke tattare a zuciyoyinsu game da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya fadin abin da ya kamata Abba ya yi bayan harin masallaci a Kano

Felix Morka ya yi musu shaguben inda ya bayyana cewa yanzu ba a san takamaimai abin da ake shirin yi ba, shin Obi ne zai koma PDP, ko Atiku ne zai koma LP?

Ya ce dama ‘yan siyasar biyu sun shahara wajen yawon siyasa, saboda haka ba abin mamaki idan sun sauya sheka.

Atiku, Kwankwaso, Obi za su hade?

A baya mun kawo mu ku labarin cewa wani jigo a jam’iyyar PDP ya bayyana cewa akwai bukatar jiga-jigan siyasar Najeriya su hada kai domin tumbuke jam’iyyar APC daga kujerar shugabancin kasar nan.

Mai magana da yawun kungiyar matasan jam'iyyar, Dare Glintstone Akinniyi, shi ne ya roki ‘yan takarar shugaban kasar nan a baya, Rabi’u Musa Kwankwaso da Peter Obi su zubar da makamansu su rungumi PDP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel