"Gwamnatin Bola Tinubu ta Jefa Najeriya Cikin Tsaka Mai Wuya," Dattijon Arewa

"Gwamnatin Bola Tinubu ta Jefa Najeriya Cikin Tsaka Mai Wuya," Dattijon Arewa

  • Dattijon Arewa kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, Farfesa Usman Yusuf ya bayyana gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ya shafe karkashin ‘yan Najeriya
  • Ya bayyana hakan a hirarsa da kafar Channels, inda ya zargi gwamnati da jefa mutane cikin fargaba da tsoro da rashin tabbas a shekara guda da Tinubu mu yi a kan mulki
  • Farfesa Usman Yusuf wanda mamba ne a kungiyar dattawan Arewa ya zargi ‘yan kwamitin farfado da tattalin arzikin kasa da sun fi kama da masu karbar haraji

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Wani mai sharhi kan harkokin siyasa kuma mamba a kungiyar Dattawan Arewa Farfesa Usman Yusuf, ya caccaki salon mulkin gwamnati mai ci da Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta.

Kara karanta wannan

An soki yadda Bola Tinubu ya kare shekaran farko a kan mulkin Najeriya

Dattijon Arewar ya bayyana cewa maimakon al’ummar kasar nan su samu kwarin gwiwa a wannan lokaci, sai gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta jefa 'yan Najeriya cikin rashin tabbas.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Dattijon Arewa ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da jefa Najeriya cikin rashin tabbas Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Channels Television ta ruwaito cewa shugaban kasar ya yi fafutukar neman zabe da taken zai karawa ‘yan kasa kwarin gwiwa wajen ci gaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu ta shekara

Dattijon Arewa Farfesa Usman Yusuf, wanda tsohon babban Sakatare ne na hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIS) ya bayyana cewa gwamnatin APC ta yaudari ‘yan Najeriya.

Farfesa Usman Yusuf ya ce shekara dayar da ta wuce shekara ce da ba komai a cikin ta sai yaudara, fatara da rashin tabbas, kamar yadda Vanguard News ta wallafa.

Tsohon babban sakataren kuma yi bulala ga kungiyar kula da tattalin arzikin shugaban kasa, yana mai bayyana mambobin a matsayin wanda suka fi kama da masu karbar haraji maimakon bunkasa tattalin arziki.

Kara karanta wannan

CNG: Manyan matakai 3 da Tinubu ya dauka na janye Najeriya daga dogara da man fetur

MDD ta jero nasarorin gwamnatin Tinubu

A baya mun kawo mu ku labarin yadda majalisar dinkin duniya (MDD) ta yabi yadda Bola Ahmed Tinubu ke gudanar da mulkin Najeriya domin ciyar da ita gaba.

Mataimakiyar Sakataren Majalisar, Hajiya Amina Mohammed ce ta bayyana hakan, inda ta ce shugaban na namijin kokari wajen inganta tsaro da farfado da tattalin arziki

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel