Mai Neman Takara a NNPP Ya Zargi Kwankwaso da 'Cinye' Masa Kudi Lokacin Zaben 2023
- Atiku Abubakar Isah ya yi sha’awar zama wakilin mutanen mazabar Ida / Ibaji / Ofu / Egalamela a majalisar tarayya
- ‘Dan siyasar ya ce shi kadai aka saidawa fam, amma aka tsaida wanda yake ya fi kashewa jam’iyyar NNPP kudi a 2023
- Atiku Abubakar ya ce dama saboda Rabiu Kwankwaso ya shigo NNPP, kuma ya ce ba zai je neman hakkinsa a kotu ba
- Matashin tsohon 'dan Kwankwasiyya ne, kafin abubuwa su canza daga baya, Legit Hausa ta yi hira ta musamman da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Atiku Abubakar wani ‘dan siyasa ne mai tasowa a jihar Kogi, ya taso jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankawso a gaba.
‘Dan siyasar ya nemi tikitin tsayawa takarar ‘dan majalisa mai wakiltar Ida/Ibaji/Ofu/ Egalamela a NNPP, sai dai bai dace ba.
Atiku ya saye fam a NNPP a 2023
Atiku Abubakar ya yi ikirarin ya saye fam a jam’iyyar NNPP domin zaben 2023, amma a karshe aka maye gurbinsa da wani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya ce shi kadai jam’iyyar NNPP ta saidawa fam ya nemi kujerar ‘dan majalisar Ida/ Ibaji/Ofu/Egalamela a zaben da ya wuce.
A cewarsa, daga baya sai ya ji wani wanda bai yanki takardar shiga neman takara ba ne ya samu tuta, bayan ya gama kashe kudi.
Atiku zai kai Kwankwaso/NNPP kotu?
‘Dan siyasar ya shaidawa Legit cewa duk abin da ake yi, ya ki ya shigar da kara a kotu kuma a karshe APC ta lashe zaben a Kogi.
Da mu ka nemi jin ko nawa ya kashe, ya ce ya batar da kusan N1.2m, amma babu abin da ya yi masa ciwo kamar bata masa lokaci.
“Mun zauna da shi (Rabiu Musa Kwankwaso), ya nuna mani ni ne ‘dan takaran majalisa.”
“Abin da ya fi bata mani rai shi ne yadda aka bar ni a je ina ta surutu cewa na samu tikiti.”
Kwankwaso da kudin fam a NNPP
Sai dai a ka’ida ba Kwankwaso yake da hakkin kula da kudin sayen fam a NNPP ba, ‘dan siyasar ya ce ya zauna da shugabannin jam’iyyar.
Atiku ya ce ya yi zama da shugabannin NNPP na kasa a lokacin, amma hakan bai sa an rage masa asarar da ya yi wajen shiga zaben ba.
Duk abin da ya faru, yana ganin sai yadda Kwankwaso ya ce ake yi a NNPP kuma tun farko saboda shi ya shigo jam’iyya mai kayan dadi.
Rikicin da za a iya yi a 2027
A rahoton nan, kun ji cewa shekara da shekaru kenan ana bakar adawa tsakanin ‘Yan darikar Kwankwasiyya da mutanen Gandujiyya.
A Kaduna, ana shuka irin rigima tsakanin Nasir El-Rufai da tsohon yaronsa a siyasa, gwamna Uba Sani bayan an fara kuka game da bashi.
Asali: Legit.ng