Abinci Ya Ƙare: Gwamna Ya Sallami Shugabannin Kananan Hukumomi 21 a Jiharsa

Abinci Ya Ƙare: Gwamna Ya Sallami Shugabannin Kananan Hukumomi 21 a Jiharsa

  • Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo ya kori dukkan shugabannin kananan hukumomi 21 da ke jihar
  • Soludo ya ba da wannan umarni ne ta bakin kwamishinan kananan hukumomi, Collins Nwanbunwanne a cikin wata sanarwa
  • Ya bukaci dukkan wadanda abin ya shafa da su mika duk wasu kayayyaki masu muhimmanci ga shugaban gudanarwa a kananan hukumominsu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Anambra - Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya sallami dukkan shugabannin kananan hukumomi 21 a jihar.

Soludo ya umarci dukkan wadanda abin ya shafa da su yi gaggawar mika dukkan wasu muhimman abubuwa ga shugabannin gudanarwar a kananan hukumominsu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya nada tsofaffin gwamnoni 4 da Ministan Buhari a manyan muƙamai

Gwamna Soludo ya sauke ciyamomin ƙananan hukumomi 21
Gwamna Charles Soludo ya sauke shugabannin kananan hukumomi 21 bayan kammala wa'adinsu. Hoto: Charles Soludo.
Asali: Facebook

Anambra: An ba tsofaffin shugabannin sabon umarni

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan kananan hukumomi, Collins Nwabunwanne ya fitar, Cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nwabunwanne ya bukaci dukkan tsofaffin shugabannin da su mika komai daga ranar Litinin 20 ga watan Mayu, cewar rahoton Punch.

"Yayin da wa'adinku ya kare a matsayin shugabannin kananan hukumomi, ana umartanku da ku mika dukkan abin da ya shafi ofisoshinku ga shugabannin gudanarwa a kananana hukumominku."
"Wannan umarni zai fara aiki ne daga gobe Litinin 20 ga watan Mayu, muna godiya da aikin sadaukarwa da kuka yi ga jiha."
"Duk wani korafi ko karin bayani za a tura ne ta hannun mai girma kwamishina."

- Collins Nwanbunwanne

Yanayin zaben kananan hukumomi Anambra

Rahotanni sun tabbatar da cewa tun a mulkin tsohon Gwamna, Peter Obi a shekarar 2014 ba a sake yin zaben ƙananan hukumomi ba sai dai nadin rikon ƙwarya.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: EFCC za ta binciki 'dan majalisa kan daukan nauyin ta'addanci

Yanzu shekaru 10 kenan tun bayan gudanar da zaben wanda har wani tsohon gwamna ya kammala wa'adinsa a jihar.

Ƴar Majalisar Tarayya ta ci zabe

A wani Labarin, kun ji cewa Tsohuwar mamban Majalisar Tarayya, Hajiya Binta Bello ta yi nasarar lashe zaben kananan hukumomi da aka yi a jihar Gombe.

Binta Bello tana daga cikin ƴan takarar jam'iyyar APC a kananan hukumomi 11 da suka yi nasarar lashe zaben da aka gudanar.

Dukkan ƴan takarar jami'iyyar 11 ne suka yi nasara da kuma kansiloli 114 a zaben da aka gudanar a ranar 27 fa watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.