2027: Tsohuwar Hadimar Buhari Ta Fadi Yadda Atiku da Obi Za Su Taimaki Tinubu Cikin Sauƙi
- Yayin da ake kokarin hada kai domin neman kwace mulki a hannun Bola Tinubu, jigo a APC ta fadi amfanin haka ga jam'iyyar
- Tsohuwar hadimar Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie ta ce hadakar Atiku da Obi za ta yi matukar ba Tinubu nasarar lashe zaben 2027
- Onocihe ta tsuguna ta roki ubangiji ya saka Atiku janyewa Peter Obi wanda ta ce zai taimakawa APC wurin lashe zaben babu wahala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohuwar shugabar kwamitin gudanarwa na hukumar NDDC, Lauretta Onochie ta magantu kan hadewar Atiku Abubakar da Peter Obi a 2027.
Onochie ta ce hadakar da za su yi za ta yi matukar ba Shugaba Bola Tinubu saukin lashe zaben 2027.
Onochie ta magantu kan hadakar Atiku, Obi
Tsohuwar hadimar Muhammadu Buhari ta yi addu'ar ubangiji ya saka Atiku na PDP ya janyewa Obi na LP takara a zaben 2027 mai zuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Onochie ta bayyana haka a jiya Asabar 18 ga watan Mayu a shafinta na X inda ta ce zai ba Tinubu damar nasara cikin sauki a zaben.
"Ina addu'ar Atiku ya janyewa Peter Obi a zaben 2027 saboda APC ta samu saukin cin zabe."
"Ka sani ban taba neman wani abu a wurinka ba saboda kullum kana ba ni abin da nake nema."
"Nagode da amsar addu'o'inmu."
- Lauretta Onochie
Atiku ya gana da Obi saboda 2027
Wannan na zuwa ne bayan ganawar Atiku da Peter Obi wanda ake tunanin suna shiri ne kan zaben 2027.
Ya ce hakan yana da matukar tasiri ga mulkin dimukradiyya wanda zai kawo ci gaba da abin da ake nema.
Atiku zai iya janyewa Peter Obi
A wani labarin, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce zai iya janyewa Peter Obi takara a zaben 2027.
Hakan ya biyo bayan wata ganawa da manyan ƴan jam'iyyun adawa suka yi a karshen wannan mako wanda bai rasa nasaba da zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng