Sanata Ya Tona Asirin Ƴan Siyasa, Ya Fadi Abin da Zai Faru Idan Ba Su Saci Dukiya Ba
- Shugaban masu tsawatarwa a Majalisar Dattawa, Ali Ndume ya fadi dalilin da yasa yan siyasa ke satar kudi
- Ndume ya ce ƴan siyasa na sata ne domin rabawa da yan mazabarsu wanda hakan ya zama musu dole saboda zabe
- Sanatan ya kuma nuna goyon bayan kan hukuncin kisa ga wadanda suka saci kudi da ya kai N1trn a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Sanata Ali Ndume da ke wakiltar jihar Borno ta Kudu ya magantu kan halin ƴan siyasa na - bera.
Ndume ya bayyana cewa ƴan siyasa da dama na satar kudin al'umma ne domin su iya rabawa da talakawansu.
Sanata Ndume ya fadi musabbabin satar kudi
Sanatan ya bayyana haka ne a yayin hira da yan jaridu game da hukuncin kisa kan masu safarar kwayoyi, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ƴan siyasa za su rasa kujerunsu idan har ba su raba kudin da suka sata ba da ƴan mazabarsu, cewar rahoton Pulse.
"Idan ka kwatanta cin hanci na ƴan siyasa da na saura, namu ya sha bam-bam saboda mutane ne suke saka ƴan siyasa sata."
"Idan kayi sata, za ka zo ne ka raba da ƴan mazabarka, idan kuma ka ki yin haka to za ka rasa damar dawowa kujerarka karo na biyu, babu amfani yin sata kenan."
"Na dade a Majalisar Tarayya, ba zai yiwu ba na ki fadan gaskiya, idan za a yi hukuncin kisa ya kamata a hada da masu cin hanci."
- Ali Ndume
Sanata Ndume ya goyi bayan hukuncin kisa
Ndume ya ce yana goyon bayan hukuncin kisa amma ba wai kawai mutum ya saci N1m ko N1bn ba, sai idan mutum ya saci N1trn zuwa sama.
Sanatan ya ce ƴan siyasar na satar ne domin rabawa da yan mazabarsu wanda hakan ba su cancanci hukunci mai tsanani ba.
Sanatoci sun kawo kudiri a Majalisa
A wani labarin, an ji cewa Majalisar Tarayya tana shirin amincewa da hukuncin kisa kan masu safarar kwayoyi a fadin Najeriya.
Majalisar ya dauki wannan mataki ne domin kawo sauyi a bangaren ayyukan hukumar NDLEA da kuma inganta lafiyar al'umma.
Asali: Legit.ng