Jigawa: Kwanaki 6 da Mutuwarsa, INEC Ta Dauki Mataki Kan Kujerar 'Dan Majalisa
- Kwanaki shida da mutuwar ɗan Majalisar Tarayya a jihar Jigawa, hukumar INEC ya ce babu kowa a kujerar
- Hukumar ta dauki wannan mataki ne bayan mutuwar Hon. Isa Dogonyaro domin shirye-shiryen sake zaben cike gurbi
- Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu shi ya tabbatar da haka a jiya Laraba 15 ga watan Mayu inda ya lissafo sauran mazabu a jihohi uku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta ce babu kujerar marigayi ɗan Majalisar Tarayya daga jihar Jigawa.
Hukumar ta ce za ta saka ranar sake zaɓen bayan mutuwar Hon. Isa Dogonyaro a ranar Juma'a 10 ga watan Mayu a Abuja.
INEC za ta shirya zaben cike gurbi
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu shi ya sanar da haka a jiya Laraba 15 ga watan Mayu a Abuja, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayin kafin rasuwarsa, ya wakilci mazabar Garki/Babura a jihar Jigawa a Majalisar Wakilai.
Farfesa Yakubu ya kuma sanar da karin wasu mazabu a jihohi uku sanadin mutuwa ko kuma murabus na masu rike da kujerun.
Sauran mazabu da INEC za tayi zaɓe
Mazabun sun hada da mazabar Khana 2 a jihar Rivers da Bagwai/Shanono a jihar Kano sai kuma mazabar Zaria Kewaye a jihar Kaduna.
Yakubu ya ce da zaran hukumar ta kammala shirye-shirye za ta sanar da lokacin gudanar da zaben a wadannan mazabu.
Ya ce nan ba da jimawa ba hukumar za ta yi martani kan sahihancin zaben ƙananan hukumomi da kansiloli a birnin Abuja.
Dan Majalisar Jigawa, Dogonyaro ya rasu
A wani labarin, kun ji cewa ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabun Garki da Babura a jihar Jigawa, Isa Dogonyaro ya rasu.
'Dan Majalisar ya rasu ne a ranar Jumu'ah da ta gabata 10 ga watan Mayu a Abuja bayan gajeruwar jinya da ya yi fama da ita.
Yar uwarsa mai suna Amina Dogonyaro ita ta sanar da rasuwar a shafinta na Facebook tare da bayyana cewa za a masa sallah a masallacin kasa da ke Abuja bayan sallar Juma'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng